Za a yi wa dan sarautar Saudiyya hukuncin kisa
Za a zartar da hukuncin kisa kan wani dan gidan Sarautar Saudiyya, wanda ya kashe wani dan kasar, kamar yadda wata jaridar kasar ta ruwaito. Wannan kuma shi ne karo na farko da ahalin gidan sarautar suka yi misalin bin doka, kan wanda duk ya yi laifi, a zartar masa da hukunci.Jaridar Arab News, da […]
Za a zartar da hukuncin kisa kan wani dan gidan Sarautar Saudiyya, wanda ya kashe wani dan kasar, kamar yadda wata jaridar kasar ta ruwaito. Wannan kuma shi ne karo na farko da ahalin gidan sarautar suka yi misalin bin doka, kan wanda duk ya yi laifi, a zartar masa da hukunci.
Jaridar Arab News, da ake bugawa cikin harshen Ingilishi, ba ta bayyana sunan wanda za a yi wa hukuncin kisan ba, amma ta bayyana cewa wani daga cikin manyan ’ya’yan gidan sarautar da ke da mukami a gwamnati, wanda shi ne Yarima mai jiran gado, “ya share fagen aiwatar da hukunci a kan yariman da ake tuhuma da kashe dan kasar Saudiyya.”
A cikin wani sako da Ministan Harkokin Cikin Gida, Yarima Mohammed bin Nayef, Yarima Salaman ya tabbatar da cewa za a aiwatar da hukuncin shari’a ba tare da nuna bambanci ba,” a cewar jaridar.
Wannan sako na Yarima Salman, ya biyo bayan sakon da mahaifin wanda aka kashe ya aiko na cewa ba zai yafe ba, kuma yana takaicin diyyar jinin dansa da aka ba shi.