Za A Yi wa Daraktocin CBN 8 Ritaya, Ma’aikata 100 Za su Koma Legas
Ana zargin korar ‘yan Arewacin Najeriya daga CBN.
Za a sallami akalla daraktoci takwas da ke aiki a Babban Bankin Najeriya CBN bisa wani dalili da har yanzu ba a gama fayyacewa ba.
Majiyarmu a bankin ta tabbatar mana da cewa wasu daga cikin wadanda za a sallamar har an miƙa musu takarda tun ranar Juma’a 15 ga Maris, 2024.
“Abin da na sani dai shi ne tabbas, wasu tun ranar Juma’a aka aika musu wasikun ritaya daga aiki.
“Sai dai abin da har yanzu ba mu tantance ba shi ne, shin ritayar ta gaggawace, ko kuma ta kawo ƙarshen yarjejeniyar aiki ce da aka kulla da su,” in ji majiyar.
Sai dai abin da majiyar ba ta fayyace ba shi ne dalilin sallamar waɗannan manyan ma’aikata daga aiki.
Kazalika, ba ta tabbatar da cewa laifi suka yi aka dakatar da su ko kuma an same su da hannu wurin aikata ba daidai ba.
- Gobara ta yi mummunan ta’adi a kasuwar babura a Sakkwato
- ’Yan bindiga sun sace mutum 87 a wani sabon hari a Kaduna
Wata majiyar kuma ta ce “ina ganin babban dalilin sallamar waɗannan daraktoci shi ne, sun yi aiki tare da tsohon gwamnan da aka tsige watannin baya, wato ana ganin kamar na hannun daman zamanin Godwin Emefiele ne.”
Tun Yammacin ranar Alhamis dai ake ta gunagunin sallamar manyan daraktocin a tsakanin ma’aikatan babban bankin.
Rashin sanar da ‘yan jarida gaskiyar abin da ke faruwa kan dalilan wannan taƙaddama na ci gaba da zama barazana ga sauran ma’aikatan bankin, domin kuwa suna ganin kamar wannan wata gobara ce da ta taso daga kogi, kuma ƙila ta shafi da yawa daga cikinsu.
Binciken Aminiya ya bankaɗo cewa wasu daga cikin daraktocin sun lashi takobin kalubalantar hukumar bankin kan sallamarsu, yayin da wasu suka ce za su fawwala wa Allah, su yi tafiyarsu domin aiki a CBN yanzu ya zama kamar aiki a kan ƙaya.
Wani da bai so mu ambaci sunansa ba ya bayyana mana cewa “ Idan har aka ba ni takardar sallama, zan karba in yi wa Allah godiya bisa damar da Ya ba ni na yin aiki a wurin, da kuma irin gudunmawar da na bayar a wurin kawai in sa takalmi na in yi gaba, in ci gaba da rayuwata.”
Ana ganin cewa bankin na shirin ɗauko waɗansu da suka yi aiki suka yi ritaya a wasu wuraren domin maye gurbin wadanda aka sallama.
Akwai rade-radin cewa za a ɗauko Mataimakin Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Hakeem Odumosu mai ritaya wanda ya riƙe matsayin Kwamishinan ‘Yan Sanda a Jihar Legas domin riƙe ɓangaren tsaro na CBN.
Zargin Cin Zarafin Wadanda Suka Yi Aiki Da Emefiele
Ma’aikatan bankin na zargin cewa sabon gwamnan bankin, Yemi Cardoso, na ƙoƙarin korar duk wani da ya yi aiki kuma yake yi wa tsohon gwamnan bankin biyayya ne kawai ta janyo wannan bita da kullin.
Zargin korar ‘Yan Arewacin Najeriya daga CBN
Kafin yanzu dai Hukumar Babban Bankin na Najeriya ta mayar da aƙalla ma’aikata 150 kula da bankunan kasar nan Legas.
Wannan dai wani ɓangare ne da ke kula da bankuna masu hada-hada a Najeriya ɗaya ne daga cikin sassa 29 na CBN.
Wannan sauyin matsuguni ga sashen ya janyo ce-ce-ku-ce, inda ake ganin hukumar bankin na yin makarkashiyar sallamar duk wani dan Arewacin Najeriya da ke aiki a CBN din.
Sai dai CBN ɗin ya musanta wannan zargi, inda ya ce hedikwatar kusan ɗaukacin bankunan Najeriya na Legas ne, don haka an maida sashen da ke lura da su wurin da su ke ne ba wani abu ba.
Ya kara da cewa, an ɗauki wannan mataki ne domin a rage cunkoson ma’aikatan da ke aiki a hedikwatarsa ta Abuja domin tabbatar da yin aiki yadda ya dace.
Zargin Daukar ‘Ya’yan Masu Hanu Da Shuni Aiki A CBN
Hukumar Babban Bankin Najeriya CBN ta bayyana cewa an ɗauki ‘ya’yan manyan kasar nan da ke da kumbar susa a bankin a lokacin jagorancin Godwin Emefiele a karkashin Gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammad Buhari.
Bankin ya ce, wadanda aka ɗauka aiki ba sa komai sai dumama kujeru a hedikwatar, da yawo tsakanin ofisoshin abokansu da ke wurin don dayawa cikinsu basu da wani abu da suke yi a hedikwatar.
Za a Mayar Da Karin Mutane 100 Aiki A Legas
Akalla ma’aikatan babban bankin na kasa ya ƙara zakulo wasu mutane dari domin turawa aiki zuwa ofishinsa na Legas.
Mun gano cewa an riga an rubuta takardar umurnin komawa aiki a ofishin bankin da ke Legas daga ranar 29 ga Afrilu na wannan shekarar.
Hukumar CBN Ta Yi Gum
Wani ƙarin abin mamaki kan wannan gagarumin mataki da bankin ya ɗauka shi ne yadda duk wani yunkuri na jin ina aka kwana kuma ina za a tashi ya zama gagara badau.
Domin kuwa duk kwakwarmu mun gaza samun Hakama Sidi-Ali da ke da alhakin magana da mu ta ce wani abu, wadda muka kira wayarta tare da aika mata sakonnin kar ta kwana amma shiru har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Yadda Wannan Aiki Ya Samo Asali
Bincikenmu ya gano cewa tun da aka ayyana Folashodun Shonubi a matsayin wanda zai rike kujer gwamnan bankin na wucin gadi, ya yi yunkurin korar duk wanda ya yi aiki da tsohon gwamnan Bankin Emefiele.
Sai dai mun samu rahoton wasu na kusa da shi sun ba shi shawara a wancan lokaci, kan cewa kar a yi gaggawar sallamar kowa, domin ba mukaman siyasa suke rike da shi ba, da har za a iya sauke su dare guda.
Majiyarmu ta shaida mana cewa da gwamnan rikon ya ga bazai iya sallamar ma’aikatan da gaggawa ba, sai ya yi hanzarin canza musu wurin zama kai tsaye, ya cire su daga hedikwatar a watan Nuwamban da ya gabata.