Za a kara albashin ma’aikata a Legas
Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi yi wa ma’aikatan jihar karin albashi ya zama wajibi saboda yanayin tsadar rayuwar.
Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya amince da yi wa ma’aikatan gwamnatin jihar karin albashi.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin raba sabbin motoci na alfarma guda 100 ga wasu daraktoci a ma’aikatun gwamnati.
- An hana ’yan jarida daukar zaman Kwamitin Amintattun PDP da Wike
- Mutum 9 ’yan gida daya sun mutu bayan cin abinci
Sanwo-Olu ya ce zuwa karshen wannan wata za a fara raba motoci ga wasu daraktocin jihar.
Ya yi albishir din ne yayin ziyarar da ya kai sakatariyar gwamnatin jihar a ranar Talata.
A cewarsa, yi wa ma’aikatan karin albashi ya zama wajibi duba da yanayin tsadar rayuwar da ake fuskanta.
Sai dai bai bayyana yawan abin da za a kara a albashin ba, ko lokacin da za a fara biya, duk da cewa ya ce an kammala dukkan tsare-tsare.
Ya nuna godiyarsa ga ma’aikatan bisa hadin kai da goyon bayan da suka bai wa gwamnatinsa tun kafuwarta zuwa yau.