Za a yi wa masana’antar fina-finai a Najeriya Inshora

Hukumar Inshora ta Najeriya ta ce ta kammala shirye-shiryen yi wa masana’antar fina-finan Najeriya inshora, saboda mutuwar bazata da ’yan fim ke yi da matsalar rashin lafiya da kuma asarar da suke yi a masana’antar.Darakta-Janar din Hukumar Mista Sunday Thomas ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kira taron ’yan jarida a makon jiya.Ya […]

Za a yi wa masana’antar fina-finai a Najeriya Inshora
Za a yi wa masana’antar fina-finai a Najeriya Inshora

Hukumar Inshora ta Najeriya ta ce ta kammala shirye-shiryen yi wa masana’antar fina-finan Najeriya inshora, saboda mutuwar bazata da ’yan fim ke yi da matsalar rashin lafiya da kuma asarar da suke yi a masana’antar.
Darakta-Janar din Hukumar Mista Sunday Thomas ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kira taron ’yan jarida a makon jiya.
Ya ce Amurka da kasashen Turai masu harkar fim da suka hada da jarumai da furodusoshi da daraktoci da masu kasuwancin fina-finai da sauransu suna da inshora, inda haka ya taimaka musu.
A harkar fim a Najeriya an rasa manyan masu harkar saboda matsalolin rashin lafiya kamar kansa da hadari, wadansu kuma an yi garkuwa da su.
Ya ce:  “A yanzu haka kwamitin da hukumarmu ta nada tuni ya kammala shirye-shirye don samar wa masana’antar fina-finan Najeriya inshora, kamar yadda takakwarorinta na kasashen Turai da kuma Amurka suke da shi. Nan da lokaci kadan za mu kawo rahoton yadda shirin zai kasance.”