Za a yi wa mata rigakafin cutar sankarar bakin mahaifa a Kano
Cibiyar Daƙile Cutar Sankara ta Kano (KCTC) ta ce a mako mai zuwa za a fara rigakafin cutar sankarar bakin mahaifa ga ’yan mata ’yan shekaru 9 zuwa 14.
Allurar rigakafi
(Daga: pixabay.com)
Cibiyar Daƙile Cutar Sankara ta Kano (KCTC) ta ce a mako mai zuwa za a fara rigakafin cutar sankarar bakin mahaifa ga ’yan mata ’yan shekaru 9 zuwa 14.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da cibiyar ta ce adadin masu fama da cutar ya kai kusan kaso 60 cikin 100 na masu fama na’ukan cutar ta kansa da ake duba su a cibiyar.
Babbar Daraktar cibiyar, Dr. Nafisa Abdu, ta bayyana hakan a ranar Asabar yayin wani shirin wayar da kan jama’a a cibiyar lafiya ta Giginyu, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano.
Ta ce yawan masu fama da cutar sankarar mahaifa ne ya sa aka yanke shawarar tashi tsaye wajen shirin rigakafin cutar da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.
“Yana da muhimmanci iyaye su kawo ’ya’yansu mata domin a yi musu rigakafi. Gwamnati ta samar da rigakafin kyauta ga ’yan mata, kuma wannan babban mataki ne wajen rage yawan masu fama da cutar sankarar mahaifa a jihar,” in ji ta.
Jami’in yaƙi da cutar sankara na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Dr. Bashir Yusuf Yunusa, ya ce za a fara rigakafin a ranar Asabar mai zuwa a matsayin wani bangare na bikin Ranar Cutar Sankara ta Duniya.
Ya ce shirin ya shafi ’yan mata masu shekaru 9 zuwa 14, kafin su fara sanin ɗa namiji, domin kare su daga kwayoyin HPV nau’in 16 da 18, wadanda ke da alaka sosai da cutar sankarar mahaifa.
“Muna fatan yi wa sama da ’yan mata 500 a unguwannin Giginyu da Badawa. Wannan makon an ware shi ne don wayar da kan jama’a, domin kawar da rashin fahimta a kan cutar da kuma karfafa karɓuwar rigakafin,” in ji shi.
Babban mai kula da maganin cutar kansa a cibiyar, Peter Emmanuel Mshelia, ya ce an zabi asibitin na Giginyu ne saboda duba al’ummar da ke makwabtaka da cibiyar ta sankara.
Ya ce nan gaba kaɗan, shirin wayar da kan jama’a zai bazu zuwa sauran al’ummomi a wasu yankunan.