Za a yi wa matashi bulala 12 kan samun sa da kodin
Wata kotun Majistare a Kano ta bada unarnin yi wa wani tela mai shekaru 20 da aka kama da kwayar Kodin bulala 12 da zaman gidan kaso na wata biyu. Alkalin kotun, Faruk Ibrahim-Umar ne ya yankewa matashin, dan unguwar Fagge, hukuncin bayan samun sa da laifin mallakar kwayar kodin, da kumar tayar da hankalin […]
Wata kotun Majistare a Kano ta bada unarnin yi wa wani tela mai shekaru 20 da aka kama da kwayar Kodin bulala 12 da zaman gidan kaso na wata biyu.
Alkalin kotun, Faruk Ibrahim-Umar ne ya yankewa matashin, dan unguwar Fagge, hukuncin bayan samun sa da laifin mallakar kwayar kodin, da kumar tayar da hankalin al’umma.
Tun da fari dai dan sanda mai gabatar da kara, Aminu Dandago, ya bayyana wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne ranar 16 ga watan Yuni a unguwar Fagge da ke Kano.
Ya kuma ce a ranar ce da karfe 9:00 na dare ’yan sandan da ke sintiri a Faggen suka kama telan da kwalaba guda ta Kodin din, laifin da ya sabawa sashi na 183 da na 391 (A) na kundin Penal Code.