Za a yi wa Tinubu, Mataimakinsa, Gwamnoni da ’yan majalisa karin albashi

Gwamnati ta ce za a yi karin ne saboda yanayin tattalin arziki

Za a yi wa Tinubu, Mataimakinsa, Gwamnoni da ’yan majalisa karin albashi

Tinubu da Shettima

Hukumar da ke Kula da Rabon Tattalin Arzikin Kasa (RMAFC), ta amince da yin karin albashi na fiye da kaso 114 cikin 100 ga zababbun ’yan siyasa da alkalai da masu rike da mukaman gwamnati.

Daga cikin wadanda za su amfana da sabon karin akwai Shugaban Kasa da Mataimakinsa, Gwamnoni da Mataimakansu da kuma ’yan majalisa da ma’aikatan bangaren shari’a.

RMAFC ce dai hukumar da aka dora wa alhakin kayyade zababbun masu rike da mukaman siyasa da Ministoci da Kwamishinoni da mashawartan Shugaban Kasa da Gwamnoni da sauran wadanda aka ambata a sassa na 84 da kuma 124 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Tuni dai hukumar ta bukaci Majalisun Dokoki na Jihohi da su gaggauta yin kwakwarima ga dokokinsu, ta yadda za a sami damar aiwatar da sabon karin.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), Shugaban hukumar ta RMAFC, Muhammadu Shehu ne ya yi kiran a Birnin Kebbi ranar Laraba, kuma ya sami wakilcin Kwamishinan hukumar, Rakiya Tanko-Ayuba.

Ya ce karin ya fara aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Janairu, kuma an yi shi ne daidai da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki.

Ya ce rabon da a yi irin wannan karin albashin tun a shekara ta 2007. Ya ce karin ya zama wajibi saboda abin da ake biyansu ya dace da yanayin tattalin arzikin kasa na yanzu.