Za a yi wa Wilshere tiyata a kafa

dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Jack Wilshere wanda ya samu rauni a shekarar 2011 a kafarsa ta hagu, likitoci za su sake yi masa aiki bayan da ya sake jin rauni a kafar.Za a yi wa Jack Wilshere tiyata inda ake sa ran zai yi jinyar wata uku idan aka kammala aikin.Wilshere ya […]

Za a yi wa Wilshere tiyata a kafa
Za a yi wa Wilshere tiyata a kafa

dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Jack Wilshere wanda ya samu rauni a shekarar 2011 a kafarsa ta hagu, likitoci za su sake yi masa aiki bayan da ya sake jin rauni a kafar.
Za a yi wa Jack Wilshere tiyata inda ake sa ran zai yi jinyar wata uku idan aka kammala aikin.
Wilshere ya sake jin rauni a cikin watan Agusta, kuma an yi hasashen zai murmure a watan Satumba, bayan kammala buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin Kofin Nahiyar Turai.
Sau biyu ana yi wa Wilshere aiki a kafarsa ta hagu a bara, bayan da ya ji rauni a karawar da suka yi da Manchester United a watan Nuwamban 2014.
Wilshere na fama da jinya a kafarsa ta hagu tun lokacin da ya gamu da raunin a 2011, inda ya yi jinyar wata 15 a lokacin.