Za a yi wa yara miliyan 1.2 rigakafin malariya a Borno

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) tana sa ran yi wa yara akalla  miliyan daya da dubu dari daya allurar rigakafin zazzabin cizon sauro domin kare su daga cutar a bana. Babbar jami’ar hukumar a Najeriya kan kula da zazzabin na malariya, Misis Iniabasi Nglass ta bayyana hakan yayin kaddamar da gangamin yaki da cutar a […]

Za a yi wa yara miliyan 1.2 rigakafin malariya a Borno

Sauro

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) tana sa ran yi wa yara akalla  miliyan daya da dubu dari daya allurar rigakafin zazzabin cizon sauro domin kare su daga cutar a bana.

Babbar jami’ar hukumar a Najeriya kan kula da zazzabin na malariya, Misis Iniabasi Nglass ta bayyana hakan yayin kaddamar da gangamin yaki da cutar a sansanin ‘yan gudun hijira na El-Miskin da ke Maiduguri.

Ta ce an shirya gangamin ne don ganin a bana cutar ba ta yi tasirin da ta saba yi a lokacin damina ba.

“Yayin gangaminmu na karshe a watan Yuli, mun yi wa yara miliyan daya da dubu dari daya rigakafin, kuma yawancinsu ‘yan shekara uku zuwa watanni 59 da haihuwa ne daga kananan hukumomi 25 na Jihar Borno,” inji Misis Iniabasi.

Babbar jami’ar ta kara da cewa shirin zai gudana ne sau hudu a cikin kwanakin marka-marka na daminar bana wanda a cikinsu ne aka fi samun barkewar zazzabin.

Ta ce rigakafin ta kan yi aiki na tsawon kwanaki 35 a jikin yaran da aka yi wa.

Yayin rigakafin watan Yuli, babbar jami’ar ta ce sun samu nasara 100 bisa 100 saboda hadin kan da iyayen yara suka ba su.

Shi kuwa babban jami’in shirin yaki da zazzabin cizon sauron a jihar, Mala Waziri, cewa ya yi a shekarar 2017, kananan hukumomi 12 ne kacal suka ci gajiyar shirin, sabanin bana da 25 suka amfana.

Ya ce kananan hukumomin Marte da Abadam ne kawai gangamin bai sami damar zuwa ba saboda matsalar tsaro.

Ya kuma yi gargadin cewa yaran da suke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar saboda sauron da ya ke cizon su.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos