Za a yi zaben kananan hukumomin Jihar Katsina ranar 2 ga Agusta

Hukumar Zabe ta Jihar Katsina ta bayyana cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar 2 ga Agusta mai zuwa, kamar yadda Kwamishinan Hukumar Zaben Alhaji Abubakar Lawal Malunfashi ya shaida wa manema labarai a ofishinsa.Kwamishinan ya ce, kamar yadda yake a sashi na 4 kashi na 2 da na 3 na […]

Za a yi zaben kananan hukumomin Jihar Katsina ranar 2 ga Agusta
Za a yi zaben kananan hukumomin Jihar Katsina ranar 2 ga Agusta

Hukumar Zabe ta Jihar Katsina ta bayyana cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar 2 ga Agusta mai zuwa, kamar yadda Kwamishinan Hukumar Zaben Alhaji Abubakar Lawal Malunfashi ya shaida wa manema labarai a ofishinsa.
Kwamishinan ya ce, kamar yadda yake a sashi na 4 kashi na 2 da na 3 na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa gyara ya nuna da kuma sashi na 4 na dokar zabe ta Jihar Katsina, hakkin hukumar ne na tsarawa da shiryawa da daukar nauyi da sa ido tare da tabbatar da aiwatar da zaben shugabanni da mataimakansu da kansiloli a kananan hukumomi 34 da ke cikin jihar. Alhaji Lawal ya ce, hukumar zaben za ta yi iya kokarinta na ganin an aiwatar da zaben kamar yadda doka ta tsara. Kuma ya yi kira ga masu ruwa da tsaki musamman jam’iyyun siyasa da magoya bayansu su ba da cikakken hadin kai tare da bin dokokin zabe don aiwatar da ingantacce kuma sahihin zabe.
Shugaban ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Barista Ibrahim Shema wadda a cewarsa ta bayar da taimako da gudunmuwar da ya kamata ta fuskar kudi.
Ya ja hankalin jam’iyyun siyasa a kan dokar da ta hana lika hotunan ’yan takara a gine-ginen gwamnati da suka hada da makarantu da turakun lantarki da sauransu. “Duk fostar dan takarar da za a lika za a yi haka kodai a ofisoshin jam’iyun siyasa ko mallakar dan takara ko waninsa,” inji shi.
Ya ce doka ta ba hukumar damar dakatar da zabe ko dage shi a rumfar zabe ko mazaba ko karamar hukuma a kan dalilin yin amfani da karfi ko aukuwar tashin hankali dalilin zaben.
Shirye-shiryen zaben kananan hukumomin jihar da suka hada da sanarwar ranar zaben da kamfe da sayar da fom ga ’yan takara da sauransu ya fara tun ranar Litinin da a gabata.