Za a zabi Gwarzon dan kwallon Duniya a ranar Litinin mai zuwa

A ranar Litinin mai zuwa 13 ga watan Janairun da muke ciki ne ake sa ran Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) za ta zabi Gwarzon dan kwallon Duniya da ake yi wa lakabi da FIFA Ballon D’or na shekarar 2013.Zaben zai gudana ne a Zurich da ke kasar Suwazilan inda ake sa ran […]

Za a zabi Gwarzon dan kwallon Duniya a ranar Litinin mai zuwa

A ranar Litinin mai zuwa 13 ga watan Janairun da muke ciki ne ake sa ran Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) za ta zabi Gwarzon dan kwallon Duniya da ake yi wa lakabi da FIFA Ballon D’or na shekarar 2013.
Zaben zai gudana ne a Zurich da ke kasar Suwazilan inda ake sa ran masu horar da kungiyoyin kwallon kafa daga sassan duniya da Kyaftin-kyaftin da masana harkar kwallo da kuma ’yan jarida za su kada kuri’unsu don zakulo wanda ya fi cancanta..
’Yan kwallo uku ne za su fafata a zaben da suka hada da Frank Ribery dan kasar Faransa da ke buga kwallo a kulob din Bayern Munich da ke Jamus da Lionel Messi, haifaffren Ajantina da ke wasa a kulob din FC Barcelona da ke Sifen da kuma Cristiano Ronaldo, haifaffen kasar Fotugal da ke buga kwallo a kulob din Real Madrid na Sifen.
Frank Ribery ya kai wannan mataki ne bayan ya taimakawa kulob din Bayern Munich lashe manyan kofuna biyar a kakar wasan da ta wuce yayin da Lionel Messi kuma ya shiga yin takara bayan ya taimakawa kulob din FC Barcelona lashe kofin La-Liga da kofin Sarki watau (Kings Cup).  Shi kuma Cristiano Ronaldo ya shiga takarar ce ganin yadda ya rika zura kwallayen da suka wuce na kowane dan kwallo a kakar wasan da ta wuce.  Kuma ya taimaka wa kasar haihuwarsa hayewa gasar cin kofin duniya bayan ya zura kwallaye uku a ragar Sweden.
Masana da dama suna rika hasashen wanda zai lashe kyautar,yayin da wasu suke ganin Frank Ribery ne ya fi cancanta wasu kuwa sun goyi bayan Lionel Messi ne yayin da wasu ciki har da Diego Maradona suka goyi bayan Cristiano Ronaldo a wajen lashe kyautar.
Lionel Messi ne dan kwallon da ya kafa tarihin lashe gasar sau hudu a jere, shi kuma Cristiano Ronaldo sau daya ya taba lasheta yayin da Frank Ribery bai taba lashewa ba.