Za ka iya watsi da sakamakon zaben da aka yi maka ta hanyar magudi?

Kwanakin baya wani mai takarar kansila a Jihar Kwara, a karkashin jam’iyyar PDP ya ki yarda da zaben da aka yi masa, saboda ya hakkake cewa abokin takararsa na jam’iyyar APC ne ya ci zaben, amma sai aka yi magudi aka juyar da sakamakon.  Filin muhawara ya leka wasu jihohi don jin ra’ayin wasu jama’a […]

Za ka iya watsi da sakamakon zaben da aka yi maka ta hanyar magudi?
Za ka iya watsi da sakamakon zaben da aka yi maka ta hanyar magudi?

Kwanakin baya wani mai takarar kansila a Jihar Kwara, a karkashin jam’iyyar PDP ya ki yarda da zaben da aka yi masa, saboda ya hakkake cewa abokin takararsa na jam’iyyar APC ne ya ci zaben, amma sai aka yi magudi aka juyar da sakamakon.  Filin muhawara ya leka wasu jihohi don jin ra’ayin wasu jama’a kan ko mutum zai iya watsi da sakamakon zaben da aka yi masa ta hanyar magudi?  Ga dai yadda ra’ayoyin suka nuna, kamar haka:

Zan iya yin watsi da irin wannan sakamakon zabe  -Ustaz Tahir Zubair
Ustaz Tahir Zubairu, Unguwar Sabo Ibadan: Ni dai, saboda tsoron Allah, zan iya yin watsi da irin wannan sakamakon zabe na bogi, domin duk abin da ka ci ko ka amfana da shi a dalilin amincewa da sakamakon bogi, to, ka ci ne ta haramtacciyar hanya. Abin bakin ciki ne, ganin cewa, mu musulmi mun yi watsi da shimfidar da addinin Islam ya yi mana tun farko a game da al’amuran da suka shafi rayuwarmu baki daya. Amma a kasashen Turai (Yahudu da Nasara) sun rungumi kwatanta gaskiya irin wacce kansila a karamar Hukumar Shawo a Jihar Kwara ya kyamata. Ya kamata ’yan siyasa su yi koyi da abin da ya faru a Jihar Kwara. Idan ana samun irin wannan matashi a harkokin siyasar kasar nan, to kuwa al’amura za su daidaita.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno