Za ka iya watsi da sakamakon zaben da aka yi maka ta hanyar magudi?1
Kwanakin baya wani mai takarar kansila a Jihar Kwara, a karkashin jam’iyyar PDP ya ki yarda da zaben da aka yi masa, saboda ya hakkake cewa abokin takararsa na jam’iyyar APC ne ya ci zaben, amma sai aka yi magudi aka juyar da sakamakon. Filin muhawara ya leka wasu jihohi don jin ra’ayin wasu jama’a […]
Kwanakin baya wani mai takarar kansila a Jihar Kwara, a karkashin jam’iyyar PDP ya ki yarda da zaben da aka yi masa, saboda ya hakkake cewa abokin takararsa na jam’iyyar APC ne ya ci zaben, amma sai aka yi magudi aka juyar da sakamakon. Filin muhawara ya leka wasu jihohi don jin ra’ayin wasu jama’a kan ko mutum zai iya watsi da sakamakon zaben da aka yi masa ta hanyar magudi? Ga dai yadda ra’ayoyin suka nuna, kamar haka:
Ba zan karba ba, in dai an yi magudi an ce ni ne na ci -Abdullahi Mohammed
Abdullahi Mohammed Rtean, Bauchi: Ra’ayina, ba zan karba ba. Shi wannan bawan Allah, ya yi ne saboda yana son gyara tsarin dimokuradiyya, don yawanci ana dora mutane ba don su ne suka ci ba. Wannan abu da ya yi, ba a taba irinsa ba. Ya nuna hali nagari, wanda ya kamata mutane su yi koyi da shi saboda mutane ba su san mene ne haramun ko hakkin wani a siyasance ba, tunda idan sun hau duk abin da suka ci haramun ne kuma abin da mutum ya samu ba zai yi albarka ba.
Don haka ya kamata duk masu karrama mutane game da abin da ya shafi dimokuradiyya, su karrama wannan mutum don ya taka rawar gani.