Za ka iya watsi da sakamakon zaben da aka yi maka ta hanyar magudi?2
Kwanakin baya wani mai takarar kansila a Jihar Kwara, a karkashin jam’iyyar PDP ya ki yarda da zaben da aka yi masa, saboda ya hakkake cewa abokin takararsa na jam’iyyar APC ne ya ci zaben, amma sai aka yi magudi aka juyar da sakamakon. Filin muhawara ya leka wasu jihohi don jin ra’ayin wasu jama’a […]
Kwanakin baya wani mai takarar kansila a Jihar Kwara, a karkashin jam’iyyar PDP ya ki yarda da zaben da aka yi masa, saboda ya hakkake cewa abokin takararsa na jam’iyyar APC ne ya ci zaben, amma sai aka yi magudi aka juyar da sakamakon. Filin muhawara ya leka wasu jihohi don jin ra’ayin wasu jama’a kan ko mutum zai iya watsi da sakamakon zaben da aka yi masa ta hanyar magudi? Ga dai yadda ra’ayoyin suka nuna, kamar haka:
Zan amince da sakamakon da aka yi magudi a cikinsa -Alhaji Bashir
Alhaji Bashir Mai Borno, tsohon kansila ne a Ibadan: kwarai da gaske, zan amince da irin wannan sakamakon da aka yi magudi a cikinsa, domin idan ka ki amincewa, to za a tafi ba tare da kai ba ne. Dalilina shi ne, tun farko da ma ba a shirya yin zaben gaskiya ba. Idan ma ka kama aiki a cikin ofis, ba wani abin alkhairi za ka tsinana ba, saboda ka shiga ofishin ne ta mummunar hanya, wacce addinan Islam da Kiristanci ba su amince ba. Kai, hatta al’adunmu na gargajiya ba su yarda da magudi ba.