Za ka iya watsi da sakamakon zaben da aka yi maka ta hanyar magudi?4
Kwanakin baya wani mai takarar kansila a Jihar Kwara, a karkashin jam’iyyar PDP ya ki yarda da zaben da aka yi masa, saboda ya hakkake cewa abokin takararsa na jam’iyyar APC ne ya ci zaben, amma sai aka yi magudi aka juyar da sakamakon. Filin muhawara ya leka wasu jihohi don jin ra’ayin wasu jama’a […]
Kwanakin baya wani mai takarar kansila a Jihar Kwara, a karkashin jam’iyyar PDP ya ki yarda da zaben da aka yi masa, saboda ya hakkake cewa abokin takararsa na jam’iyyar APC ne ya ci zaben, amma sai aka yi magudi aka juyar da sakamakon. Filin muhawara ya leka wasu jihohi don jin ra’ayin wasu jama’a kan ko mutum zai iya watsi da sakamakon zaben da aka yi masa ta hanyar magudi? Ga dai yadda ra’ayoyin suka nuna, kamar haka:
Zan iya watsi da sakamakon zaben -Mohammed Hassan
Muhammada Hassan danbaza: Ni a ra’ayina shi ne zan iya watsi da sakamakon zaben da aka zabeni,kuma nasan banci zaben ba,amma sai idan nasan cewa banyi asara da yawaba,amma idan nayi asara da yawa to zan karba don nin rage zafi, soda kasan siyasa a kasannan bashi yiwuwa sai kanada kudi, musamman ma idan wadannan kudinrantosu nayi daga wani ko banki.