Za mu ƙwace aiki titin Abuja-Kano daga Julius Berger —Minista
Umahi ya ce idan kamfanin bai amince da tayin gwamnati na Naira biliyan 740 a matsayin kuɗin aikin ba, za ta ƙwace kwangilar
Ministan Ayyuka, David Umahi ya ba wa kamfanin Julius Berger wa’adin kwana bakwai kan aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Kano.
Umahi ya ce idan kamfanin bai amince da tayin gwamnati na Naira biliyan 740 a matsayin kuɗin aikin ba, za ta ƙwace kwangilar cikin makonni biyu ta ba wa wani kamfani da zai iya.
Ministan ya ce Julius Berger ya jima yana jan kafa a kan aikin kuma tun shekarar 2013 ake tattaunawa da shi a kan kuɗin aikin amma ya ki amincewa.
Ya ƙara da cewa, majalisar zartarwa ta kasa ta amince a biyan biliyan N740 a kan gyaran ɓangaren aikin da ke hannun Julius Berger wanda a baya aka tsada biya da kuɗin tsarin bashin haraji.