Za mu ɗauki mataki idan zanga-zanga ta wuce gona da iri — Sojoji

An gargadi masu fakewa da zanga-zangar suna sace-sacen kayan gwamnati da al’umma.

Za mu ɗauki mataki idan zanga-zanga ta wuce gona da iri — Sojoji

Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya ce sojoji za su dauki muddin zanga-zangar tsadar rayuwa da ke ci gaba da gudana a faɗin ƙasar ta wuce gona da iri.

Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin da yake gargadin masu fakewa da zanga-zangar suna ɓarna da sace-sacen kayan gwamnati da al’umma.

Ana iya tuna wasu bata-gari sun fake da zanga-zangar wajen wawushe kayayyaki a wata cibiyar Hukumar Sadarwa ta Nijeriya NCC tare ƙona wasu sassanta a jihar Kano.

Wasu bayanai na cewa an shirya ƙaddamar da cibiyar fasahar sadarwa a mako mai zuwa.

Sai dai da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, Janar Musa ya buƙaci masu zanga-zangar da su gane cewa ɓarna ba ta da amfani kuma zai jefa al’ummar ƙasar cikin ruɗani.

Yayin da yake yaba wa rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa ƙoƙarin da take yi na tabbatar da zaman lafiya, ya ƙara da cewa za a tilasta wa sojoji shiga lamarin idan har aka ci gaba da samun tashin hankali.

Janar Musa ya roki ’yan kasar da su kasance masu sanin ya kamata a lokacin da suke zanga-zangar kamar yadda doka ta ba su dama.

“Muna so mu faɗakar da waɗanda suke ɓarnatar da dukiya, cewa ba za mu naɗe hannayenmu mu ga an lalatar da ƙasarmu ba.

Janar Musa ya kara da cewa gwamnati na bakin kokarinta wajen magance matsalolin tattalin arziki da ke damun kasar, yana mai kira ga jama’a da su riki gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da alhakin nauyinsu.

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara