Za mu amince da tsarin a kasa a tsare – Jega

Shugaban Hukumar zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya ce hukumarsa za ta amince da tsarin nan na a kasa a tsare a raka, muddin dai za su kasance cikin tsari da bin doka. Ya ce hakan za ta iya faruwa kuma a amince, kamar yadda aka amince a zabubbukan 2011. […]

Za mu amince da tsarin a kasa a tsare – Jega

Shugaban Hukumar zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya ce hukumarsa za ta amince da tsarin nan na a kasa a tsare a raka, muddin dai za su kasance cikin tsari da bin doka. Ya ce hakan za ta iya faruwa kuma a amince, kamar yadda aka amince a zabubbukan 2011.

Shugaban ya fadi haka ne a yayin ganawa ta musamman da ya yi da ’yan jarida da masu ruwa da tsaki kan al’amuran kasar nan, a Abuja.
Haka kuma ya mayar da martani ga wasu mutane da kungiyoyi da suke ta yin kiran a sauke shi daga mukaminsa, inda ya ce ba ya cikin matsi daga kowa cewa sai ya sauka, don haka ba zai yi murabus daga mukaminsa ba, domin kuwa yana da aikin da zai gudanar.
Shugaban ya ce ya gamsu da yanayin tsaron da ake da shi, musamman a Arewa maso gabashin kasar nan a yanzu, kamar kuma yadda ya ce babu wata damuwa game da masu zabe idan suka zabi su tsaya sauraren sakamako.
Yayin gudanar da taron ganawar, wanda cibiyar Reinbent Media tare da hadin gwiwar cibiyoyin Ford Foundation da Kuka Centre suka shirya, Jega ya ce “Ina da aiki a gabana don haka zan maida hankali domin tabbatar da cewa na gudanar da shi zuwa karshe.”
Da aka tambaye shi cewa ko yana fuskantar matsin cewa sai ya sauka daga mukaminsa, Jega ya amsa da cewa “Ba na fuskantar wani matsi daga kowa cewa sai na sauka daga mukamina. Idan ma har na ce zan sauka, ban yi wa kaina adalci ba, domin kuwa ina da aiki a gabana kuma zan maida hankali domin kammala shi.”
Jega kuma ya karyata jita-jitar da ake yadawa, cewa wai zai tafi hutun aje aiki. “Ya kamata mu gane cewa, shi irin wannan hutu ne da ake bayarwa ga ma’aikacin da ke gabanin ajiye aiki kuma mutum na da zabin ya tafi ko kar ya tafi. Kamar yadda na fadi da farko, ina da aiki a gabana har zuwa 11 ga Afirilun bana; don haka wannan hutun ba ya gabana. Babu wani mahaluki da ya ce mani in tafi hutu. Ina dai jin wannan jita-jita ne a jaridu.” Inji Shugaba Jega.
Hukumar Zaben dai ta ta’allaka irin wadannan kiraye-kiraye na cewa Jega ya sauka daga mukaminsa ga wasu ’yan siyasa, domin cin ma wata manufa a siyasance. “Ina sanar da al’ummar Najeriya cewa, akwai abubuwa da yawa da ake fada, wadanda ba gaskiya ne ba, ana fadin su ne kawai da nufin kawar da hankulan jama’a.” Inji Jega.
Da aka tambaye shi bayani game da matsayin sabuwar jam’iyyar nan ta YDP, sai ya bayyana cewa koda ba a yi wa jam’iyyar rijista ba, babu abin da zai shafi zabubbukan da ke tafe a ranakun 28 ga watan nan da kuma 11 watan gobe.
Ya kara bayyana cewa hukumarsa tuni ta daukaka kara game da hukunci babbar kotun ta tarayya, sannan kuma ya ce ita kanta kotun ta bayyana cewa hukuncin da ta zartar bai ce a saka jam’iyyar cikin zabubbukan da ke tafe ba.
Farfesa Jega kuma ya ce, duk da cewa bai da cikakken shirin yin bayani game da al’amuran tsaro dangane da zabe, amma duk da haka ya ce “Mun gamsu sosai da yanayin tsaro kafin ma a dage zabubbukan da aka yi a baya.”
Da yake bayani game da shirin da hukumarsa ta yi game da zabe mai gabatowa, sai ya ce: “Mun shirya sosai domin gudanar da zabubbukan nan kuma za mu gamsar da bukatun ’yan Najeriya.” Ya kuma yi roko ga ’yan siyasa da cewa su daina karkatar da hankulan mutane game da zaben.
Game da na’urar tantance masu zabe da hukumar ke son yin amfani da ita a zaben mai zuwa, Jega ya ce: “Mun shirya tsaf domin gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana, zabe mai gamsarwa kuma na gaskiya, wanda ya dara na 2011 inganci.” Ya nemi al’umma da su amshi sabon tsarin zaben na amfani da na’ura da fahimta.
Haka kuma ya yi karin bayani game da amfani da jami’an tsaro na ’yan sanda a tashoshin zabe. Ya ce kowace rumfa za a samar da jami’an ’yan sanda guda uku, amma kuma ya kara da cewa babu dan sandan da zai kasance dauke da makami.