Za mu ba hukumomin yaki da cin hanci hadin kai – Gwamnatin Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta ci gaba da bai wa hukumomin yaki da cinn hanci da rashawa hadin kai da goyon baya domin binciken duk wani zargin na almundahanar kudi ta yadda za a cimma nasarar yaki da cin hanci da kuma almubazzaranci da dukiyar gwamnati.Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba […]
Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta ci gaba da bai wa hukumomin yaki da cinn hanci da rashawa hadin kai da goyon baya domin binciken duk wani zargin na almundahanar kudi ta yadda za a cimma nasarar yaki da cin hanci da kuma almubazzaranci da dukiyar gwamnati.
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai dangane da wata gayyata da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta yi wa wasu manyan jami’an gwamnatin jihar domin ganawa da su kan batun kudin kananan hukumomi da ake zargin an barnatar har fiye da Naira biliyan uku.
Malam Muhammad Garba ya ce gwamnatin Jihar Kano tana shirye domin bai wa hukumomin yaki da cin hanci da ke kasar nan cikakken goyon baya da hadin kai domin ganin an cimma nasarar da ake bukata na magance almundahana da kudin jama’a, inda ya yi fata jama’a za su yi wa lamarin kyakkyawar fahimta.
Idan dai za a iya tunawa, wani mai suna Injiniya Ali Maishanu ne ya rubuta wani korafi ga Hukumar ICPC yana kalubalantar gwamnatin jihar dangane da wasu kudi da ya yi zargin cewa an dauka daga asusun kananan hukumomin jihar 44 kuma aka taimaka wa wani dan takarar Shugabancin kasa wanda ba a bayyana sunansa ba.
Cikin jami’an gwamnatin da aka gayyata zuwa ofishin ICPC har da Sakataren Gwamnatin Jihar Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi da Babban Akantan Jihar Alhaji danjuma Mahmoud da Kwamishinan kananan Hukumomi na Jihar Alhaji Murtala Sule Garo da manyan sakatarorin ma’aikatun kudi da na ayyyuka.