Za mu bai wa masu zanga-zanga kariya —Shugaban ’yan sanda

Sufeton ya yi alƙawarin bai wa masu zanga-zangar kariya.

Za mu bai wa masu zanga-zanga kariya —Shugaban ’yan sanda

Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya umarci manyan jami’an ’yan sanda su bai wa waɗanda za su yi zanga-zanga daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024 kariya.

Wannan na zuwa ne biyo bayan buƙatar wani lauya mai kare haƙƙin ɗan adam, Ebun-Olu Adegboruwa, na a samar da tsaro ga masu zanga-zangar.

Sufeton ya umarci jami’an ‘yan sanda a faɗin Najeriya su tabbatar da tsaron masu zanga-zangar.

Wasiƙar, wacce Mataimakin Sufeton, CP Johnson Adenola ya sanya wa hannu, ta kuma gayyaci Adegboruwa zuwa wani taro a Abuja ranar 30 ga watan Yuli, 2024, domin tattaunawa kan yadda zanga-zangar za ta wakana.

Hukumomi, ciki har da ’yan sanda, sojoji, da Hukumar Tsaro ta DSS, sun gargaɗi jama’a kan irin zanga-zangar da aka yi a Kenya.

’Yan siyasa suna fargabar cewa zanga-zangar na iya zama kamar ta EndSARS wadda aka yi a watan Oktoban 2020.

Hakan ya sa suka roƙi matasa su dakatar da shirin zanga-zangar.

Duk da haka, matasan sun kafe kan cewar zanga-zangar za ta gudana, wadda ke nuna rashin jin daɗinsu kan halin matsin tattalin arziƙi da ake fuskanta a ƙasar.

An shirya gudanar da zanga-zangar a dukkanin jihohin ƙasar, har da babban Birnin Tarayya, Abuja yayin da ‘yan ƙasar ke fama da tsadar kayan abinci da hauhawar farashin kayayyaki.

Matsalar tattalin arziƙi na da nasaba da manufofin gwamnati na cire tallafin man fetur da kuma kasuwar musayar kuɗi, wanda ya haifar da ƙaruwar farashin abinci da kayan masarufi.

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe

Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka

TikTok ya daina aiki a Amurka