Za mu bai wa ministoci horo kan kishin kasa – Abubakar Tsanni

Alhaji Abubakar Tsanni shi ne babban darakta na kungiyar fafutikar sanya kishin kasa a zukatan ’yan Najeriya da aka kaddamar  kwanakin baya, ya bayyana irin kudororinsu tare da mayar da martani ga masu gangamin cewa an ware sashin kudu maso gabas a Najeriya, da kuma sauran bayanai.Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Ko za ka […]

Za mu bai wa ministoci horo kan kishin kasa – Abubakar Tsanni
Za mu bai wa ministoci horo kan kishin kasa – Abubakar Tsanni

Alhaji Abubakar Tsanni shi ne babban darakta na kungiyar fafutikar sanya kishin kasa a zukatan ’yan Najeriya da aka kaddamar  kwanakin baya, ya bayyana irin kudororinsu tare da mayar da martani ga masu gangamin cewa an ware sashin kudu maso gabas a Najeriya, da kuma sauran bayanai.Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ko za ka gabatar da kanka?
Abubakar A. Tsanni: Sunana Abubakar A Tsanni.  Ni ne babban darakta na Think Nigeria First Initiatibe (TNFI), kungiya ce ta fafutikar sanya kishin kasa a zukatan ’yan Najeriya a duk inda suke.
Aminiya: Me ya karfafa muku gwiwar kafa wannan kungiya?
Abubakar A. Tsanni: Makasudin kafa wannan kungiya ita ce cusa sha’anin kishin kasa ga al’ummar Najeriya a cikin dukkan al’amuransu, kuma a duk inda suka samu kansu. Wata rana na yi tafiya zuwa kasar Amurka inda na sauka a New York, na ziyarci gidan wani dan Najeriya dan asalin jihar Jigawa, ina wasa da wani dansa sai na tambaye shi kai dan wane kasa ne, budan bakin yaron sai ya ce mini ni ba Amurke ne, na ji takaicin hakan, amma cikin raha sai na ce kai dan Najeriya ne. To wannan na daga cikin abin da ya ba ni karfin gwiwa na jagoranci kafa wannan kungiya, kuma AlhamduliLahi, a yanzu haka muna da mambobi da ke wakiltarmu a dukkan yankunan nan shida na Najeriya.
Aminiya: To ta wace hanya kuke bi wajen cin ma muradunku?
Abubakar A. Tsanni: Muna amfani da hanyoyi daban- daban, kamar shirya gangami da kuma laccoci ga nau’ukan al’umma daban-daban, ga kuma kafofin sadarwa. A yanzu haka muna da niyyar shirya horo na musamman ga sabbin ministoci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zaba  don kira da kuma jaddada masu muhimmancin kishin kasa a dukkan al’amuransu, tare da sanya shi a matsayin abu na farko a zukatansu, da kuma yi wa kasa aiki ba don arzuta kawunansu ba, sai don fitar da kasar nan daga cikin kangin da ta samu kanta a ciki.
Aminiya: Wata matsala da ta bullo kai a yanzu haka ita ce ta neman a raba kasa da wasu matasa daga sashin kudu maso gabas ke neman a yi, me za ka ce a kan wannan?
Abubakar A. Tsanni: Rashin kishin kasa da kuma yarda da muhimmancin ko wane sashi na  Najeriya shi ya jawo mana wannan. Dole mu yarda da cewa kowane sashi na Najeriya na bukatar wani sashi, kuma kasancewarmu a hade shi ne karfinmu da kuma kimarmu a idon duniya. Yadda wadansu yankunan kudu ke tallafawa da arzikin mai, haka nan yankin arewa ke tinkaho da wajen noma wanda da shi ne a ke ciyar da kasar baki daya. Kuma ya kamata su wadannan matasa da yawancinsu ba a haife su ba a lokacin da aka yi yakin basasa ko kuma ba su yi wayo ba a lokacin su sani, shi kansa wanda ya fara jagorartar fafutikar tsagerancin, wato Ojukwu, ya yi nadamar al’amarin, tare da nuna rashin fa’idarsa, kamar yadda ake ta yayatawa ta hanyoyin sadarwa a yanzu.
Aminiya: Wace hanya kake ganin ya kamata a bi don shawo kan al’amarin, ta lalama ce ko kuma da karfi?
Abubakar A. Tsanni: Lalama ita ce zabin farko, a kira su domin a yi sulhu, a nuna masu matsalar hakan, a kuma nuna masu cewa abin da yawancin jihohinsu ke samu a matsayin kason kasa ya dara na wadansu yankunan, idan kuma batun ba da mukamai ne, to ai yanzu ne ma aka fara rabawa, kwamitin da zai zabi mambobi da shugabannin cibiyoyin gwamnati yanzu ne ya fara aiki, idan ko lalacewar hanyoyinsu ne suke korafi a kai, to ai idan ba su koka wa gwamnatin da ta shekara goma  sha shida ba, ba su da dalilin kokawa wadda a yanzu ne ta cika wata shida, inda ko wadanda za su yi aikin ma, wato ministoci, a yanzu ne aka zabe su, ina ganin dai tsoron kar a maimaita fifikon da aka ba su ne a baya a kan sauran bangarori na Najeriya ya sa su ke wannan bore, kuma na tabbata shugaba Buhari ba zai yi irin wannan son kai ba.
Aminiya: Me za ka ce a kan yaki da cin rashawa da wannan gwanatin tasa a gaba wanda jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ana nuna son kai a ciki?
Abubakar A. Tsanni: Kodayake mu ba ’yan siyasa ba ne, amma dai a gaskiya idan ka ji irin barnar da a ka tafka a baya dole ka goyi bayan wannan yaki na kwato dukiyar kasa, abun akwai takaici kwarai, wata dukiyar da a ka sata zuwa kasar waje shi kansa wanda ya satan ba lallai ya san adadinta ba, sannan karin abun takaicin, yana mutuwa shi ke nan iyalansa kansu ba su san ta yadda za su kai gareta ba. Watakila dai PDP na wannan korafi ne saboda ’ya’yanta ne suka fi fuskantar al’amarin, wannan kuma ba abin mamaki ba ne, idan aka yi la’akari da cewa ’ya’yantan nan su ne suka fi rike wurarare na musamman a gwamnatin da ta gabata, wadda kuma a kanta ne aka fi karfafa wannan bincike.