Za mu biya halastattun ma’aikata ne kawai ba na boge ba – Namashaya Diggi

Shugaban karamar Hukumar Kalgo, Alhaji Umaru Namashaya Diggi ya bayyana cewa duk wanda ba ma’aikacin halas ba ne a karamar hukumar, ba zai samu albashinsa ba na wannan watan. Shugaban ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya kammala wata ganawa ta sirri da ya gudana tare da Mai Martaba Sarkin Gwandu, Dakta Muhammadu […]

Za mu biya halastattun ma’aikata ne kawai ba na boge ba – Namashaya Diggi

Shugaban karamar Hukumar Kalgo, Alhaji Umaru Namashaya Diggi ya bayyana cewa duk wanda ba ma’aikacin halas ba ne a karamar hukumar, ba zai samu albashinsa ba na wannan watan.

Shugaban ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya kammala wata ganawa ta sirri da ya gudana tare da Mai Martaba Sarkin Gwandu, Dakta Muhammadu Ilyasu Bashar da daraktocin karamar hukuma da iyayen kasa da kuma kansiloli da kuma sauran masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Kalgo. Taron ya gudana ne a sakatariyar karamar hukumar, makasudin shirya ganawar domin neman hadin kai don daidaita matsalolin da ya tarar a karamar hukumar tasa.

“Ba zan taba amincewa da duk wani ko wata a ma’aikatan boge ba a karamar hukumar Kalgo ko dan wanene, daga wannan watan na Satumba da muke ciki duk wanda ba ma’aikacin halas ba ne a karamar hukumar ba zai samu albashin sa ba, domin na fito da wani fom wanda zai bayyana ma’aikacin gaskiya, yace abin takaici ne da ban mamaki kan yadda aikin karamar hukuma ya lalace saboda son rai da ake sawa a aikin gwamnati, saboda haka ne ba zan yadda da hakan ba a wannan karamar hukuma,” in ji shi.

“A matsayina na shugaban karamar hukumar Kalgo ba zan amince da wannan tsarin biyan albashin dubu biyar ba da na tarar a lokacin da na karbi madafun iko. Ya zama wajibi a matsayina na zababben shugaba in yi iya kokarina na ganin cewa na dawo da martabar aikin karamar hukumar kamar yadda ka’idar aikin gwamnati ta ke da yardar Allah.”

Ya ci gaba da cewa, ba zai lamunci yadda wasu ma’aikata ke karbar albashi kawai ba tare da aikin komai ga karamar hukumar ba, tare da cewa, insha Allahu zai gyara wannan matsala ta yadda kowane ma’aikaci za a dubi matsayinsa na aiki, idan ba ya bisa ka’ida za a daidaita masa zama kamar yadda doka ta tanada akan aikin gwamnati.