Za mu biya Julius Berger N280bn don kammalan titin Abuja zuwa Kano —Minsita

A kowane wata za a biya kamfanin Julius Berger Naira biliyan 20 har na tsawon watanni 14

Za mu biya Julius Berger N280bn don kammalan titin Abuja zuwa Kano —Minsita

Aikin gyarar hanyar Abuja zuwa Kano mai tsawon kilomita 375

Gwamnatin Tarayya za ta riƙa biyan kamfanin Julius Berger Naira biliyan 280 domin kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kano.

Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa a duk wata za a biya kamfanin Naira biliyan 20 har na tsawon watanni 14 domin kamfanin ya kammala aikin kilomita 82 na ɓangaren ya rage a titin.

Ministan ya sanar da biyan wannan Naira biliyan 280 ne a yayin da yake kokawa kan ƙarancin kuɗaɗen gudanar da ayyukan hanyoyin.

Ya bayyana haka ne a wani zama da ya yi da Julius Berger kan ayyukan kwangilan manyan tituna da kamfanin yake gudanarwa, waɗanda Gwamnatin Tinubu ta gada.