Za mu biya sabon albashin naira 22,500- Gwamnoni
Bayan kammala ganawar gaggawa da Gwamnonin jihohin Najeriya suka yi saboda bukatar kungiyar kwadago na biyan karancin albashi sun yanke shawarar biyan naira dubu 22 da 500 maimakon dubu 30. A jiya Talata ne kungiyar kwadagon ta gudanar da gangamin karin mafi karancin albashi na naira dubu 30. Bayan kammala ganawar shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya […]
Bayan kammala ganawar gaggawa da Gwamnonin jihohin Najeriya suka yi saboda bukatar kungiyar kwadago na biyan karancin albashi sun yanke shawarar biyan naira dubu 22 da 500 maimakon dubu 30.
A jiya Talata ne kungiyar kwadagon ta gudanar da gangamin karin mafi karancin albashi na naira dubu 30.
Bayan kammala ganawar shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya Abdul’aziz Yari Abubakar kuma Gwamnan jihar Zamfara ya bayyana wa mmanema labarai cewa, ganawar ta amince da karin albashin ne saboda kar kudin ya haura rabin adadin kudin shigar kowa ce jiha.