Za mu bullo da tsarin mafi karancin albashi a tamaula —UEFA
Idan har kungiyoyi biyar za su ci nasara a koda yaushe to babu ma’ana.
Hukumar Kwallon Kafar Turai UEFA na fatan bullo da tsarin mafi karancin albashi a fagen kwallon kafar Turai yayin da dukkanin kungiyoyi suka amince kan batun.
Shugaban UEFA Aleksander Ceferin ya ce ya yi magana da hukumar Tarayyar Turai game da batun kuma an tattauna kan kawo irin wannan matakin.
- Manchester United za ta yi wa Harry Kane tayi mai gwabi
- Zaben Adamawa: Kotu ta kori karar da Binani ta shigar
“Manyan kungiyoyi, kananan kungiyoyi, kungiyoyin kwallon kafa da ke karkashin kulawar gwamnati, kungiyoyin manyan ‘yan kasuwa, kowa ya amince,” in ji Ceferin.
Shugaban FIFA Gianni Infantino ya yi magana game da yiwuwar samar da tsarin mafi karancin albashi a bangaren kwallon kafa a watan Maris.
“Ba wai muna maganar wadanda suka mallaki kungiyoyi ba ne, ana maganar darajar gasar ne, domin idan har kungiyoyi biyar za su ci nasara a koda yaushe to babu ma’ana kuma,” in ji shugaban UEFA.
“Amma dole ne ya zama yarjejeniya ta gama gari kowace da zata kunshi kowacce gasa da kuma UEFA, domin idan muka yi shi kuma sauran kungiyoyin ba su yi ba, to hakan ba shi da ma’ana.
“A yanzu, muna da sabuwar doka bayan 2024 cewa za ku iya kashe kusan kashi 70 cikin 100 na kudaden shiga don biyan albashi da hada-hadar ‘yan wasa, amma hakan bai wadatar ba saboda idan kudaden shiga sun kai biliyan biyar, kashi 70 na da yawa.
“Don haka wannan ita ce ci gaba a nan, kuma ba na jin tsoron masu kungiyoyin kwallon kafa. Uefa ce ke jagorantar gasar Turai kuma muna da kyakkyawar alaka da da hadakar kungiyoyin wasanni a halin yanzu.