Za mu canja duk zababben da ya kasa yi wa al’ummarsa aiki – dan Maliki
Dushewa da rashin kwarjini da PDP ta samu ya janyo mata tunanin neman martaba ko ta halin kaka, wanda hakan ya kai ta ga yayata cewar mambobin APC na canja sheka zuwa gare ta domin PDP ta rasa kalma daya da za ta bata APC da shi, ta neman hanyar da za ta samu amincewar […]

Dushewa da rashin kwarjini da PDP ta samu ya janyo mata tunanin neman martaba ko ta halin kaka, wanda hakan ya kai ta ga yayata cewar mambobin APC na canja sheka zuwa gare ta domin PDP ta rasa kalma daya da za ta bata APC da shi, ta neman hanyar da za ta samu amincewar mutane, shi ya sa suke kirkirar cewa magoya bayan APC na canja sheka zuwa PDP.
Ma’ajin Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Musa dan Malikin Kabi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu na Jihar Kebbi a sakatariyar jam’iyyar da ke Birnin Kebbi.
dan Maliki ya cigaba da cewa ‘ya’yan Jam’iyyar APC dake da rijista har yanzu ba su samu rahoto daga wata mazaba ba cewar mambobin APC sun bar jam’iyyar ba, ya ce wannan yakewa da PDP ke yi illa soki burutsu ne illa PDP na ganin yadda take rasa magoya baya a shiyoyin da suke ganin suna da karfi musamman bangaren inyamurai da kudu maso gabas da kuma kudu maso kudu dan nan ne PDP ke da karfi a kasar nan.
Ya ce idan kana kallon talabijin ka ga yadda dubban magoya bayan PDP suke canja sheka zuwa APC, misali a Jihar Katsina, Neja, Zamfara, Edo-Ekiti da sauran wadansu jihohin kasar nan kuma duk akan gayyaci yan’ jarida suna daukar labarai, tunda PDP ke cewa ta karbi masu canja sheka sau nawa ka taba ganin an nuna a talabijin, rediyo ko jarida, wannan abin da take yi borin kunya ce kawai.
“Yanzu haka a Jihar nan a kwanakin baya mun yi babban kamu, inda tsohon Gwamna Sa’idu Dakingari da tsohon Ministan harkokin kasashen waje, Dakta Sa’idu Balarabe Sambawa da kuma Ambasada Isah Muhammad Argungu da dubban magoya bayansu suka dawo APC daga PDP, kuma dama wadannan mutane sune PDP a Jihar Kebbi saboda haka yanzu anan Kebbi PDP ta karkare mutuwa baki dayanta.”
Wadansu Jam’iyyu suna yin hadin gwiwa wai zasu karbi mulki ne a hannun APC akan gaza cika alkawuran da ta yi ko an kasa yi wa jama’a abin da ya kamata, amma a yanzu a halin da Najeriya ke ciki, da halin da talakan kasar nan ke ciki na samun cigaba ta fannoni da dama, na tabbata duk wani mutumin da ke cikin APC ya koma PDP ko wata jam’iyyar gambiza ya yaudari kan shi ne, in kuma kana cikin PDP to ka gaggauta barin ta tunda wuri kafin jirgin nan ya cika a shiga da kai,” in ji shi.