Za mu ceto yara 48 da ’yan ta’adda suka sace a makaranta — Zulum
Zulum ya tabbatar wa mazauna yankin Mussa cewa ana ci gaba da ƙoƙari tare da sojoji da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da an ceto waɗanda aka sace lafiya.
Gwamnan Borno Babagana Zulum
Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum, ya ziyarci garin Uba don jajanta wa ]iyaye da masu kula da yaran makaranta 48 da aka sace a ranar Juma’a da ta gabata a yankin Mussa na Ƙaramar Hukumar Askira/Uba ta jihar.
Zulum ya tabbatar wa mazauna yankin Mussa cewa ana ci gaba da ƙoƙari tare da sojoji da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da an ceto waɗanda aka sace lafiya.
Gwamna Zulum, wanda ya saba ziyartar al’ummomin da rashin tsaro ya shafa don jajantawa ga waɗanda abin ya shafa da kuma tantance halin da ake ciki da kansa, ya kuma gana da iyayen yaran da aka sace a Fadar Sarkin Uba.
Da yake jawabi a wurin taron, gwamnan ya miƙa jajensa ga Sarkin, iyayen yaran da aka sace da kuma dukkan mutanen Masarautar Uba kan lamarin da ya faru.
- An kashe matashi, an jikkata wasu 12 bayan zaɓen fid-da-gwanin APC a Sabon Gari
- Tirela ta halaka ’yar sanda da wani mutum a Gombe
Gwamnan ya ƙara da cewa: “Ina tabbatar muku cewa Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu, da gwamnatin Jihar Borno za su yi duk mai yiwuwa don tabbatar da sakin yaran.”
Gwamnan ya yaba wa sojoji da sauran hukumomin tsaro saboda ɗaukar matakan kariya don hana sake taɓarɓarewar yanayin tsaro a yankin.
Ya bayyana cewa an riga an tura kwamandan Birged, manyan Jami’in ’yan sanda da sauran shugabannin hukumomin tsaro don ƙarfafa tsaro da kuma sauƙaƙe dawo da yaran da aka sace lafiya.
Zulum ya kuma yi alƙawarin ƙarfafa tsaro a Askira, Uba da yankunan da ke maƙwabtaka da su don hana sake afkuwar irin wannan lamari.
“Mun yi ƙoƙari sosai don daidaita Askira, Uba da al’ummomin da ke maƙwabtaka da su ta hanyar ƙarfafa tsaro a waɗannan yankuna,” in ji shi.
Gwamnan ya yi kira ga waɗanda suka sace yaran da su saki yaran da ba su ji ba ba su gani ba, yana mai cewa su ƙanana ne waɗanda ke buƙatar kulawa da kariya daga iyayensu.
Ya kuma yi kira ga mazauna Masarautar Uba da dukkan al’ummar Jihar Borno da su ƙara himma wajen addu’o’i, musamman a cikin kwanaki 10 na farko na watan nan na Dhul Hijjah da ake ciki.