Za mu ci gaba da kare Najeriya- Buratai

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce za su ciga da tabbatar da tsaro da kariyar Najeriya da ‘yan Najeriya. Buratai ya bayyana hakan ne bayan wani gumurzu da aka yi tsakanin sojoji da ke bataliya da 145 a Damasak da Boko Haram, inda sojojin suka fatattaki ‘yan Boko Haram […]

Za mu ci gaba da kare Najeriya- Buratai
Za mu ci gaba da kare Najeriya- Buratai

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce za su ciga da tabbatar da tsaro da kariyar Najeriya da ‘yan Najeriya.

Buratai ya bayyana hakan ne bayan wani gumurzu da aka yi tsakanin sojoji da ke bataliya da 145 a Damasak da Boko Haram, inda sojojin suka fatattaki ‘yan Boko Haram din tare da yi musu mummunar barna.

‘Yan Boko Haram din suka kawo wa sojojin harin, kamar yadda rahoton ya nuna a ranar Laraba da misalin karfe 6 na yamma, amma da misalin karfe 11 na dare aka watattake su bayan sojojin sun ci karfinsu.

Buratai ya kai ziyara Damasak, sannan daga can ya nufi Gudumbali, inda yake ci gaba da kai ziyara ga sojojin da ke yaki a yankin domin karfafa musu gwiwa.