Za mu dauki fansar dakarun da aka kashe a Neja — Rundunar Soji

Za mu yi farautar ababen zargin ta kowacce hanya.

Za mu dauki fansar dakarun da aka kashe a Neja — Rundunar Soji

Rundunar Sojin Najeriya ta ce za ta dauki fansa dangane da dakarunta da aka kashe ranar 14 ga watan Agusta a kan titin Zungeru zuwa Tegina da ke Jihar Neja.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ne ya bayyana hakan yayin jana’izar dakaru kimanin 20, waɗanda ’yan ta-da-ƙayar-baya suka kashe cikin Jihar Neja.

Da yake jawabi a maƙabartar sojoji da ke Abuja, Janar Christopher Musa ya ce babu wanda zai kuɓuta cikin waɗanda ake zargi da aikata kashe-kashen.

Ya jaddada cewa rundunar za ta yi farautar ababen zargin ta kowacce hanya.

Daga cikin manyan jami’an gwamnati da suka halarci jana’izar, akwai sabon Ministan Tsaro Badaru Abubakar da takwaransa Karamin Ministan Tsaron Najeriya, Bello Matawalle.

Wakilinmu ya ruwaito cewa a cikin waɗanda aka binne a maƙabartar har da: Farabiti Habib Aliyu da Las Kofur Nura Mohammed da AB Suleiman da Las Kofur Sunday Okopi da kuma ƙarin sojoji guda 16.

Aminiya ta ruwaito rundunar na cewa a farkon makon jiya ne aka kashe dakarunta guda 36 a lokacin wani harin kwanton-ɓauna a kan titin Zungeru zuwa Tegina kafin daga bisani wani jirgin helikwafta ya rikito ƙasa a kusa da ƙauyen Chukuba na Karamar Hukumar Shiroro duk dai a cikin Jihar Neja.

Yau za a yi jana’izar Janar Lagbaja

NAJERIYA A YAU: Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025