Za mu dauki mataki kan wadanda suka kai wa alkali hari a Gombe —Lauyoyi

An ruwaito wasu gungun mutane ne suka yi wa alkalin dukan kawo wuka a jihar.

Za mu dauki mataki kan wadanda suka kai wa alkali hari a Gombe —Lauyoyi

Lauyoyi

Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) reshen Jihar Gombe ta lashi takobin ganin an hukunta wasu wadanda suka kai wa alkalin babbar kotun jihar tare da ma’aikatansa hari suka sassare su.

Shugaban kungiyar a jihar, Barista Benjamin Sati, ya ce muddin irin haka na faruwa da akalai da ma’aikatan kotu, to kasar nan babu wanda zai tsira.

Sanarwar da ya fitar bayan zuwa biyar alkalin da ma’aikatan nasa da aka yi wa duka aka sassare shi, ta nuna rashin jin dadinsu kan wadanda suka yi masa wannan danyen aiki.

“Usman Yahaya, wanda ya ji mummunan rauni yana samun sauki, muna kira ga mambobin kungiyarmu da kada su fusata, su bai wa shugabani hadin kai wajen bin lamarin a hankali don cimma nasara,” in ji Sati.

Ya bukaci hadin kan dan sanda mai bincike na ofishin ’yan sanda da ke garin Talasse wanda zai sanar da ofishin kwamishinan ’yan sanda abin da ya faru ta hannun babban jami’i mai kula da sashen shari’a wanda yana cikin tawagar da suka kai ziyarar.