Za mu duba kudurin da zai ba Sarakuna aikin yi a gwamnatance — Abbas
Ya yi alkawarin ne a fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya
Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, ya yi alkawarin cewa majalisarsu za ta sake duba kudurin da zai bai wa masu rike da sarautun gargajiya ayyukan yi a cikin Kundin Tsarin Mulki.
Ya bayyana haka ne ranar Asabar, lokacin da ya ziyarci Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli a fadar shi da ke Zariya a Jihar Kaduna.
- Matar Dahiru Mangal ta rasu
- Abubuwan da za a iya yi da kudin tallafin man fetur na wata daya da aka cire
Ya ce ya kai ziyarar ce domin yin godiya, neman tabarraki da kuma addu’a daga Sarkin.
Tajuddeen, wanda shi ne dan majalisar da ke wakiltar mazabar Zariya a majalisar, ya samu rakiyar wasu mambobi da shugabannin majalisar yayin ziyarar.
Wannan ce dai ziyararsa ta farko zuwa mazabar ta shi, tun bayan darewarsa shugabancin majalisar.
A cewar Kakakin, “Mun kuma zo nan ne domin mu nemi shawararku, a matsayinku na iyayen al’umma masu rike da sarautun gargajiya.
“Ina kuma tabbatar maka cewa za mu sake duba kudurin da masu rike da sarautun suka mika wa majalisa suna neman aiki a Kundin Tsarin Mulki sannan mu tabbatar ya zama doka,” in ji shi.
Da yake mayar da jawabi, Sarkin na Zazzau ya ce masu rike da sarautun gargajiya sun taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba kasa kafin da kuma bayan samun ’yancin kai, don haka suna da matukar muhimmanci.
Malam Ahmed Bamalli ya kuma nuna takaicinsa kan yadda ya ce wasu ’yan siyasa sun nuna adawarsu da shirin tun da farko saboda tsoron kada a yi musu kishiya.