Za mu fadakar da Fulani muhimmacin zama wuri daya – Miyetti Allah
Matsalar makiyaya da manoma tsohuwar matsala ce wadda rashin adalci ya kawo, domin a shekarun da suka gabata makiyaya na da burtulai da aka kasa inganta su saboda sakaci har mutane daban daban a wadansu wurarare suka zo suka mamaye su, tun daga wanda gwamnati ta sani a jadawalinta da ma wadanda ba ta sa […]
Matsalar makiyaya da manoma tsohuwar matsala ce wadda rashin adalci ya kawo, domin a shekarun da suka gabata makiyaya na da burtulai da aka kasa inganta su saboda sakaci har mutane daban daban a wadansu wurarare suka zo suka mamaye su, tun daga wanda gwamnati ta sani a jadawalinta da ma wadanda ba ta sa a ciki ba, hanyoyin shanu da muke da su a lokacin da ya gabata wasu sun zama gidajen mai wasun gidajen mutane, a halin yanzu hanyar shanu zuwa mashaya ta mutu, ba a fitar da wata ba.