Za mu fallasa biliyoyin kudin da muka kwato daga gwamnatin Jonathan – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce za su fallasa yawan kudin da suka kwato daga gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ga jama’ar kasa. Shugaba Buhari ya bayyana haka ne domin mayar da martani kan zargin da Kakakin Jam’iyyar PDP na kasa Olisa Metuh ya yi cewa Shugaban kasar yana kokarin sace dukiyar kasar ne […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce za su fallasa yawan kudin da suka kwato daga gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ga jama’ar kasa.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne domin mayar da martani kan zargin da Kakakin Jam’iyyar PDP na kasa Olisa Metuh ya yi cewa Shugaban kasar yana kokarin sace dukiyar kasar ne ta hanyar cewa gwamnatin da ta gabata ba ta bar masa ko kwabo a asusu ba.
Shugaba Buhari ya ce an barnata biliyoyin Naira a karkashin mulkin Jonathan kuma za a kwato su a fallasa ga jama’a sannan a mayar da su asusun gwamnati.
Wata sanarwa da ta fito daga Mashawarcin Shugaban kasa kan harkokin watsa labarai, Femi Adesina, ta ce Buhari ya ce gwamnatinsa ta fara kankama kuma ta kuma fara haifar da da mai ido.
Sanarwar ta ce, gaskiya za ta bayyana a lokacin da aka fallasa irin kudin da aka sace da suka kai biliyoyin Dala bayan kwato su tare da mayar da su asusun tarayya.
“Nan da kankanen lokaci bayan duk tsare-tsaren gwamnatin nan ya kankama tare da fara samar da dai mai ido, ’yan Najeriya za su gano wane ne yake yi musu hidima yadda ya kamata da kuma wane ne ya mayar da su gaulaye. Lokaci kankane zai bayyana,” inji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa Olisa Metuh da mai gidansa “za su yi nadama” a lokacin da aka fara fallasar.
Shugaba Buhari ya ce barnar da gwamnatin da ta gabata ta yi ana ci gaba da magance ta, inda ya ce babu dalilin da Jonathan zai tafiyar da harkokin kasar nan kamar yadda ya yi.
Ya ce kusan dukkan bangarori da suka shafi rayuwar kasarmu sun sukurkuce kuma za a dauki lokaci kafin a gyara abubuwan da aka lalata. “Kuma wannan ne abin da gwamnatin Buhari take kokarin yi,” inji shi.
Ya ce “Al’ummar kasar nan ne gaba daya suka hadu domin kawar da gwamnatin da ta durkusar da kasar nan tana kokarin hallaka ta. Kuma ’yan Najeriya sun yanke shawarar ba za su sake barin wata gwamnati da za ta rarraba kawunansu kan dalili na yanki ko addini ko kabilanci ba.”
A makon jiya ne Shugaba Buhari ya ba shugabannin wata kungiyar Arewa tabbacin cewa gwamnatinsa za ta kwato kudin da aka sace tare da taimakon kasashen Amurka da Turai. Kafin nan Buhari ya ce ya iske asusun kasar nan fanko lokacin da ya hau mulki, da’awar da tsohon Ministan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Abubakar Olanrewaju Sulaiman, ya musanta.