Za mu fara bai wa dalibai rancen kudin karatu a watan Janairu — Tinubu

Tinubu ya ce zamanin yajin aiki a bangaren ilimi a Najeriya ya zo karshe.

Za mu fara bai wa dalibai rancen kudin karatu a watan Janairu — Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce zamanin yajin aiki a bangaren ilimi a Najeriya ya zo karshe yayin da gwamnatinsa za ta fara aiwatar da shirin bai wa dalibai lamunin karatu a watan Janairun 2024.

Tinubu bayyana haka ne a wannan Litinin din yayin da yake jawabi a wajen taron shekara-shekara na tattalin arzikin Najeriya karo na 29, wanda Kungiyar Tattalin Arzikin Najeriya (NESG) ta shirya a Otel din Transcorps Hilton, Abuja.

Shugaban, wanda ya yi magana game da tsare-tsaren gwamnatinsa na daidaita tattalin arzikin kasar tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, musamman masu zaman kansu, ya jaddada bukatar a gaggauta bullo da shirin ba da lamuni mai dorewa wanda zai taimaka wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun a watan Yunin da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya rattaba hannu a kan dokar da za ta bai wa daliban manyan makarantu bashi su yi karatu, su biya daga baya.

Ya ce za a rika adana kudaden da za a yi amfani da su wajen aiwatar da shirin ne a lalitar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, kuma za a rika bayar da su ne kawai ga daliban manyan makarantu masu karamin karfi.

Dokar dai ta tanadi bayar da bashi mara ruwa ga daliban manyan makarantu marasa karfi ta hanyar Asusun Tallafa wa Ilimi na Najeriya.