Za mu fara watsa shirye-shirye kai tsaye daga Najeriya – Shugaban Africa TB
Dokta Habib Tijjani Tahir shi ne Shugaban Shirye-Shirye da Tsare-Tsare na Gidan Talabijin na Africa TB Group da ke kasar Sudan. A tattaunawar da Aminiya a Kafanchan, ya bayyana nasarori da kalubalen da suke fuskanta: Mece ce alakarka da Africa TB? Sunana Dokta Habib Tijjani Tahir, Shugaban Shirye-Shirye da Tsare-Tsare na gidan Talabijin na Africa […]
Dokta Habib Tijjani Tahir shi ne Shugaban Shirye-Shirye da Tsare-Tsare na Gidan Talabijin na Africa TB Group da ke kasar Sudan. A tattaunawar da Aminiya a Kafanchan, ya bayyana nasarori da kalubalen da suke fuskanta:
Mece ce alakarka da Africa TB?
Sunana Dokta Habib Tijjani Tahir, Shugaban Shirye-Shirye da Tsare-Tsare na gidan Talabijin na Africa TB da ke kasar Sudan. Ni nake shugabantar sashen Hausa da Swahili da Amharic, wato Africa TB group wanda aka fara a shekarar 2009. Akwai Africa TB 1 da ya kunshi harsunan Amharic da Oromo da Tigree da kuma Afari da sauransu. Sai Africa TB 2 da ake yada shi da harshen Swahili, sannan sai Africa TB 3 da ya kunshi harsunan Hausa da Yarbanci da Fulatanci. Ni ne shugaban tsare-tsare da shirye-shiryensu gaba daya.
An haife ni a garin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna a nan na yi makarantar firamare da karamar sakandare a GSS Kafanchan a shekarar 2002 kafin in wuce makarantar Albayan da ke Jos in kammala babbar sakandare a shekarar 2005.
Bayan na kammala sai na wuce International Unibersity of Africa da ke Sudan inda na samu digiri na farko kafin in koma Jami’ar Sudan Unibersity of Science na yi digiri na biyu, a lokacin ne na fara aiki da gidan Talabijin na Africa TB3. A yanzu haka na kammala digiri na uku.
A wace shekara aka fara gudanar da wannan tasha?
An fara watsa shirye-shirye a wannan tasha ta Africa TB 3 a ranar 1 ga Janairun 2013, amma kafin nan an fara da gwaji ta hanyar saka zallar karatun Alkur’ani ana nuna fassararsa da Hausa a 2012.
Kasancewar ka kwashe shekaru da yawa a Sudan daga karatu zuwa aiki, yaya za ka kwatanta rayuwar ’yan Najeriya da ta mutanen Sudan?
To gaskiya akwai wasu dabi’u masu kyau da suka dauki hankalina kuma na yi fatan ina ma ’yan Najeriya za su zamo haka. Duk da cewa babu jama’ar da ba ta da irin nata matsalar amma abin da ya fi ban sha’awa ga mutanen Sudan shi ne karamci. Cikin kankanen lokaci za ka ga sun rike ka kamar kun dade tare. Idan aka ce an fara azumin Ramadan sukan bude gidajensu duk wanda zai wuce sai su kira shi ya yi buda baki tare da su. Wadansu kuma kan fito da tabarma ne duk wanda zai wuce sai su gayyace shi ya yi buda baki tare da su. Wadansu da garuruwansu ke kan hanya kuwa za ka ga idan masu motoci suka zo wucewa daidai lokacin buda baki sai su cire rawunansu su kama gefe da gefe suna tare motoci don mutane su fito su yi buda baki.
Kamar kaso nawa ne ke amfani da harshen Hausa a kasar?
Akwai kabilu da yawa a kasar Sudan; Larabawa da wadanda ba Larabawa ba, sai dai abin da zai fi ba ka mamaki shi ne Hausawa na daga cikin manyan kabilun kasar wadanda aka kimanta za su kai kimanin miliyan takwas. Duk da za ka ji a wasu lokuta suna gwama Hausar da wasu kalmomi na Larabci amma dai suna daga cikin kabilun da suka fi kowa yawa a kasar.
Kasancewar mafiya yawan masu kallo ko sauraronku daga Najeriya suke, ba ku yunkurin bude wani ofishi a Najeriya don saukaka al’amuranku?
Gaskiya muna da tunanin haka domin a wannan ziyara da na zo Najeriya ma yana daga cikin abin da muka tattauna, wato bude ofishi a Jihar Kano, wanda yanzu haka ma mun kammala yi masa rajista nan gaba kadan za mu bude don bai wa jama’a damar turo korafe-korafensu da shawarwari don dadada musu da kuma kusanto da su.
A bangaren talabijin, wane kalubale ne kuke fuskanta yanzu?
Matsala ta farko ita ce yadda tashar take Sudan amma malaman da ke shirye-shirye a tashar mafi yawansu daga Najeriya ne domin idan ana maganar harshen Hausa to Najeriya da Nijar aka fi tunani kafin sauran, kamar Kamaru da Ghana. Hakan ya sa yawancin shirye-shiryen ba kai-tsaye ake gabatarwa ba, sannan abu na biyu shi ne yadda mutane ke son su rika bugo mana waya kai-tsaye amma mutane na tsoron kirarmu saboda irin kudin da ake cajinsu domin lambar ta waje ce ba layin Najeriya ko na Nijar ba, kuma mutane na kokawa a kan haka.
Amma muna godiya ga Allah domin wadannan matsalolin sun zo karshe, albishir da za mu yi wa masu kallonmu shi ne a yanzu haka mun gama shiryawa tsaf yadda za mu fara gabatar da shirye-shirye kai-tsaye kuma za mu fara ne da gabatar da Hudubar Juma’a daga Babban Masallacin Juma’a na Abuja, inda za mu rika nunawa a lokacin da ake yi daga baya sauran shirye-shiryen su biyo baya. Sannan batun layin kira shi ma za mu bude layuka na Najeriya da ba za a rika cire kudi mai yawa ba don bai wa masu sauraronmu damar bayar da shawarwari ko yin tambayoyi.
To yawancin shirye-shiryenku na addini ne ko akwai tunanin sako wasu shirye-shirye domin daukar hankalin jama’a?
Eh, to shi wannan talabijin a matsayinsa na Musulunci sai mu ce ya shafi komai na rayuwa kama daga kasuwanci zuwa shugabanci da tarbiyya da zamantakewa, kowanne muna tabowa. Kusan tasha ce da ta dace da kowa babba da yaro namiji da mace wanda za ka iya kallo tare da iyali ba wata fargaba.