Za mu fara yi wa al’ummar Musulmin duniya fina-finan da suka dace da addininsu’

Wani fitaccen jarumi, mai fitowaa fina-finan Amurka kumakwararre a fina-finan barkwanci,Omar Regan, ya bayyana cewa a cikinshekarar nan shi da abokan sana’arsa zasu fara fitar da fina-finan da suka dace daal’ummar Musulmin duniya.dan fim din, wanda ya sha alwashinfitar da irin wannan fim na farko mai taken‘American Shari’ah’ (Shari’ar Amurka) abana, ya ce lokaci ya […]

Za mu fara yi wa al’ummar Musulmin duniya fina-finan da suka dace da addininsu’

Fostar fim din Da’irar Halalywood, American Shari’a da zai fito a banaWani fitaccen jarumi, mai fitowa
a fina-finan Amurka kuma
kwararre a fina-finan barkwanci,
Omar Regan, ya bayyana cewa a cikin
shekarar nan shi da abokan sana’arsa za
su fara fitar da fina-finan da suka dace da
al’ummar Musulmin duniya.
dan fim din, wanda ya sha alwashin
fitar da irin wannan fim na farko mai taken
‘American Shari’ah’ (Shari’ar Amurka) a
bana, ya ce lokaci ya yi da duniyar Musulunci
za ta fara fitar da fina-finan halal, wadanda
suka saba wa na shaidana da suka cika
duniya.
Akwai al’ummar Musulmi sama da
biliyan daya a duniya, ga shi kuma babu
wani mai shirya fim da ya kula da akidarsu
ko labarin da ya dace da su a fim.” Inji Omar
Regan, wanda Musulmi ne dan Amurka,
a yayin da yake neman al’umma su tallafa
masa domin cika burinsa na tabbatar da
da’irar shirya fina-finan Musulunci don
Musulmin duniya, wacce ya kira da taken
‘Halalywood.’
“Ya zuwa yanzu dai na yi bankwana
da da’irar shirya fina-finan Amurka
(Hollywood), zan tsunduma cikin da’irar
fina-finan Musulunci (Halalywood).” Omar
ya kara bayani.
Kamar yadda ya fada wa ’yan jarida,
Omar, wanda ya taka rawar gani a fitaccen
fim din ‘Rush Hour 2’ ya ce ya kuduri
aniyar kawo canji a da’irar shirya fina-finai
a duniya, musaman domin ganin cewa
fina-finan halal sun kawo sauyi a duniya.
Ya ce fina-finan da da’irar Halalywood za
ta rika shiryawa za su barranta da irin na
Amurka, wadanda ke bayyana Musulmi da
Musulunci a matsayin ’yan ta’adda.
“Babban kudurinmu shi ne mu samar
da kafar nishadantarwa wacce Musulmin
duniya za su yi alfahari da ita. Haka kuma
muna son mu rika fadakar da al’ummar
duniya hakikanin mene ne Musulunci kuma
wane ne Musulmi, ba kamar yadda a baya
ake yi musu mummunar fahimta ba.
“Haka kuma, wannan da’ira ta
Halalywood za ta kasance wani bagire da
marubuta da ’yan wasa da daraktocin fim
Musulmi za su baje kolinsu. Bagiren da za
su samu dama da ’yancin tsara labarunsu
da suka dace da addininsu ba tare da ana
kyamar su ko korar su ba.” Inji Omar.
Da yake kara bayani game da fim din
‘American Shari’ah’ wanda da’irar tasu za
ta fitar a bana, ya ce fim din yana dauke
ne da barkwanci a daya bangare, a yayin
da wani bangaren kuma yake dauke da
tayar da kwanji. Ya ce fim din na nuna irin
yadda mahukuntan Amurka ke amfani da
kinayar tsoratar da mutanen duniya game
da Musulunci, da nufin nema wa kansu karfi
da tasiri a duniya.
Duk da cewa ba wannan ne karo na
farko da Musulman Amurka suka fara
kafa da’irar nishadantarwa don Musulmi
ba, amma dai Halalywood ta fitar da salo
na musamman, da ta karkata alkiblarta
zuwa fina-finan Musulunci. Idan za a iya
tunawa, a 2003, mawaki Sami Yusuf ya
samu nasarar fitar da faifan wakokinsa
na fadakarwa da wayar da kai dangane
da Musulmi da addinin Musulunci. Shi
ma mawakin Musulunci, Maher Zain ya
fitar da nasa faifan wakokin a 2008, wanda
haka ke nuna cewa lallai an samu kafa ta
musamman a harkar nishadantarwar
duniyar Musulm