Za mu farfado da masakun Najeriya —Minista

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na farfado da masaku da nufin bunkasa noman auduka da samar da tufafi da kuma rage dogaro da kayan sakashen waje

Za mu farfado da masakun Najeriya —Minista

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na farfado da masaku da nufin bunkasa noman auduka da samar da tufafi da kuma rage dogaro da kayan sakashen waje.

Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Doris Nkiruka Uzoka-Anite, ta ce hakan ya hada da samar da injina da fasahohin zamani ta yadda bangaren zai iya fitar da kayyayi zuwa ko’ina a fadin duniya.

A cewar minisatar aiki ya yi nisa wajen zawarcin masu zuba jari a bangaren domin cim ma wannan manufa.

Doris ta sanar a wani zauren tattaunawa da masu harkar auduga da ya gudana a Abuja cewa, farfado da masakun zai samar a ayyuka 200,000 a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Ministar ta jaddada cewa hakan zai bunkasa samun kudade ga masu harkar dinki da zayyana da manoman aduka, baya ga samar da cigaba a bangaren samar da tufafi a cikin gida.

A nasa bangare, shugaban kunigiyar masu amfanin gona (FACAN), Sheriff Balogun, ya jaddada bukatar hadin kan duk wadanda abin ya shafa domin magance matsalolin da ke ci wa masaku tuwo a kwarya.

A cewarsa, yiwuwar fitar da tufafin da aka samar a Najeriya zuwa kasashen waje ya nuna muhimmancin samun goyon bayan masu ruwa da tsarki, kamar yadda kamfanin Dangote ya rage farashin man dizel da matatar man Dangote ta yi.