Za mu fitar da mutum miliyan 100 daga talauci – Mataimakin Shugaban kasa
Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ja hankalin masu yawan sukar wannan gwamnati da su san cewa akwai manyan kalubale da suka daibaibaye kasara nan wadanda suka hada da mutum miliyan 110 da suke fama da kuncin talauci. da muke kokarin fitar da su daga talaucin ta hanyar taimaka wa kananan masa;antu da daukar […]
Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ja hankalin masu yawan sukar wannan gwamnati da su san cewa akwai manyan kalubale da suka daibaibaye kasara nan wadanda suka hada da mutum miliyan 110 da suke fama da kuncin talauci. da muke kokarin fitar da su daga talaucin ta hanyar taimaka wa kananan masa;antu da daukar matasa aikin koyarwa da bai mata kananan ‘yan kasuwa bashi.
Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana haka ne a wurin taron laccar shekara-shekara da kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya gudanar a jiya Alhamis a Abuja.
Ya ce, “Wadansu mutane suna ta sukar gwamnati kamar yadda shi ma ya sha yi a baya, amma sai ga shi yana zama Mataimakin Shugaban kasa kuma a lokacin da jama’a da ita kanta kasar ke cikin fatara da rashin kudin shiga da faduwar farashin man fetur a duniya.”
Farfesa Osinbajo ya ce duk da kyakkyawar shirin da suke da shi na son fitar da mutane daga fatara da rashin zaman lafiya da rashin aiki da wutar lantarki da sauransu, tilas su fuskanci kalubalen da talauci da rashin kudin shiga da suke yi wa kasar nan barazana.
Farfesa Osinbajo, ya kara da cewa ya dace mutane su san cewa bai kamata a hada ci gaban kasashe kamar Tanzaniya da Rwanda da wasu suka yi a wurin taron da na Najeriya ba. Ya ce akwai lale, domin in aka hada yawan mutanen Tanzaniya da na Rwanda ba su kai rabin mutanen Najeriya ba. Sannan kudin shigan kasar Tanzaniya bai kai kashi daya bisa shida na kudin shigar Jihar Legas ba. Sannan Rwanda tana da karancin jama’a in da ba ta kai a hada ta da wata jihar ba a Najeriya.
A jawabin maraba da baki, Shugaban Kamfanin, Malam Kabir Yusuf ya ce, taken wannan taro na bana shi ne: “Shekara Hamsin Bayan Juyin Mulki: Shin Najeriya tana ci gaba?” Ya ce juyin mulkin ya janyo Yakin Basasa, kuma ya bata rawar kasar nan da tsalle.
Alhaji Kabiru Yusuf ya ce ’yan Najeriya sun iya sukar wani, maimakon ganin laifin kansu, kuma ya ce mafita ga kasar nan ita ce yadda za a kula da inganta rayuwar jama’a, don haka lokacin yin mulki kawai ya wuce, “Saboda ya dace a kashe cin hanci da rashawa domin a inganta harkokin kasuwanci a samu a dauki mutane aiki gadan-gadan,” inji shi.
A jawabin Shugaban Taron Malam Adamu Fika, Wazirin Fika ya ce: “Mun saba da mulki na Firayi Minista amma aka dora wa ’yan Najeriya mulkin Shugaba Mai cikakken iko, wanda ba mu san shi ba, ba kuma za mu san shi ba. Mafita ga kasar nan ita ce mu koma ga tsarin mulki irin na Firayi Minista.”
A mukalar da ya gabatar a wurin taron, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya) ya hori ’yan jarida su rika bincike mai zurfi kan duk labarin da za su buga, sannan ya bukaci a tallafa wa wannan gwamnati ta Shugaban Muhammadu Buhari don ta kai kasar nan ga gaci
Da take tofa albarkacin bakinta a wurin taron Dokta Mairo Manadara ta ce, ya kamata Najeriya ta yi koyi da kasar Rwanda inda su ma suka yi Yakin Basasa amma yanzu aikin gina kasa ne a gabansu ba nuna bambance-bambance ba.