Za mu gina makekiyar masana’anta ta zamani don nakasassu – Hamza Waziri Mohammed

Hamza Waziri Muhammad  Nakasasshe ne, kuma shi ne Shugaban kungiyar da ke kare hakkin Nakasassu a  Jihar Bauchi. Ya zanta da manema labarai a Bauchi jim kadan bayan aza harsashin  gina masana’antar Wanke Mota irin ta zamani ta nakasassu  a jihar, inda ya bayyana matsalolin da ke damun nakasassu a Najeriya, musamman a Arewa, da […]

Za mu gina makekiyar masana’anta ta zamani don nakasassu – Hamza Waziri Mohammed

Hamza Waziri Muhammad  Nakasasshe ne, kuma shi ne Shugaban kungiyar da ke kare hakkin Nakasassu a  Jihar Bauchi. Ya zanta da manema labarai a Bauchi jim kadan bayan aza harsashin  gina masana’antar Wanke Mota irin ta zamani ta nakasassu  a jihar, inda ya bayyana matsalolin da ke damun nakasassu a Najeriya, musamman a Arewa, da sauran al’amura. Ga yadda hirar ta kasance:

Ga ka sanye da kayan masu yi wa kasa, wato NYSC ka kammala karatunka ne?

Na kammala digirina na farko yanzu haka ina digiri na biyu, na dai yi karatu na kwasa-kwasai da dama, amma na kai ga kammala karatun nawa ne a fannnin kasuwanci ‘Business Administration’ yanzu a daidai wannan lokacin ina koyarwa a kwalejin Tatari Ali Polytechnic da ke Bauchi a matsayin mai yi wa kasa hidima.

Mai  digiri yakan so yin aikin gwamnati ba tare da taimaka wa wasu ba; kai mai ya baka sha’awar taimakon ‘yan uwanka?

Ni a zahirin gaskiya ma da ka ganni ba na son aikin gwamnati, na fi son kawai in fita in yi gwagwarmayar kasuwanci. Yanzu da nake  yi maka magana ni ne  shugaban kammafanin (COE) na HWM ‘Global Edport and Inport LTM.’ Kamfanina ne da na mallaka, wanda na ke safarar kayan abinci daga kasashen waje zuwa Najeriya da kuma Najeriya zuwa kasashen waje. Tabbas nakasa ba gazawa ba ce, domin kuwa don ina da nakasa ba shi ne zai hanani shiga a dama da ni ba. Babu yadda za a yi barewa ta yi gudu danta ya yi rarrafe, ni na tashi na ga mahaifiyata tana kasuwanci, duk da mahaifina shi ba dan kasuwa ba ne, ma’aikacin gwamnati ne. Ko yanzu ka je gidanmu za ka samu mahaifiyarmu tana saida pure water. Tun ina dan shekara 16 na ke kasuwanci, ni manomi ne kuma dan kasuwa ne.

 Idan aka ka kammala wannan masana’anta wadanne irin nakasassu za ka dauka? 

Kowane jinsi za mu hadu da ita domin yin aiki, domin dukkaninmu muna da kalubale, ka ga yanzu da muke kaddamar da fara wannan aikin, ga shugaban makafi digiri biyu yake da shi Masters digiri. , akwai shugaban kurame, shugaban kutare ne kawai bai zo ba. Kowane jinsi za mu hada su waje guda domin kowa ya samu abun dogaro da kai. Domin na ga wani abin al’ajabi, na je wajen taro na ga makaho da kurma suna magana ka ga wannan baiwa ce Allah ya yi mana, wannan fa ba ya gani, wannan kuma ba ya ji amma na ga suna sadar da magana a tsakaninsu, ka ga baiwa ce daga Allah. Shi Allah ba ya zaluntar bawanSa, wani hanin ga Allah baiwa ne, kurma da makaho suna hira.

Wace manufa ta sa kake kokarin gina Cibiyar ayyuka ga nakasassu? 

Hakika yau mun aza tubalin gina masana’antun da za mu yi domin taimaka wa junanmu. Mutanen da Allah ya jarrabe mu da nakasa, kuma , ni shugaban wannan cibiyar ne na assasa da kaina, domin taimaka wa ‘yan uwana masu nakasa. Manufar kafa wannan cibiyar dai shi ne domin mu dauki ma’aikata ‘yan uwanmu nakasassu mu samar musu da aikin yi, domin dogaro da kai, sannan zan yi kokari a duk watan in rika biyan kowane ma’aikacin wannan masana’antar tawa a kalla Naira dubu 18.

Wadannne irin Sana’o’i masu nakasa za su rika yi domin dogaro da kansu?

Daga cikin sana’o’in akwai sana’ar wankin mota na zamani, wanda babu irinsa a Jihar Bauchi, tare da kawata shi. Saboda wannan muhallin da aka ba mu nawucin gadi ne, don haka ba wai za mu gine wajen ga baki daya baya. A’a za mu kewaye wajen mu yi masa kawa, wato ado ke nan, ta yadda kowa zai yi sha’awar kawo motarsa, domin mu wanke masa, sannan za mu gyara wani gefe  namu da furannin kallo (filawowi) na kawa domin jawo hankalin abokan huldarmu. Ina kuma tabbatar maka idan Allah ya sa mun kammala a duk fadin Jihar Bauchi ba za a yi wata masana’antar wanke mota da ta kai wannan tamu ta nakasassun wanda muke fadi tashin samar da ita a halin yanzu.

 Me zai sa ya zama haka?

Dalilin da zai zama babu irinsa shi ne kayyakin aikin da irin Injunan wanke motar ba ma a kasar nan na saye su ba. Babu irin wadannan injunan yau a fadin Jihar Bauchi ga baki daya, injina ne masu nagarta. Abin dai sai kun gani kawai, idan Allah ya sa suka bar mu muka kai ga kammala gyara wajen sana’armu ta nakasassun. Idan sun bar mu fa ke nan. Domin yanzu haka muna hasashen sawun giwa yana neman danne na rakumi.

Me ya faru?

Eh-to mun dora tubalin aikin wannan masana’artar, kamar yadda na fada maka, sai kuma ga wata takarda ta biyo bayanmu daga can ma’aikatar raya birane ta jiha (SDB) wai mu dakatar da wannan aikin, alhali fa tun kafin mu kai ga fara wannan aikin mun riga mun samu amincewar ma’aikatar filaye da safiyo ta Jihar Bauchi. Na shaida wa SDB cewar mu fa ba mu kai ga fara wannan aikin ba sai da muka samu izini daga ma’aikatar filaye, na shaida musu ga yadda aka yi ga yadda aka yi, ni dalibi ne mai son bin doka. Don haka na je ma’aikatar filaye na shaida musu, na kuma je hukumar raya biranen SDB, sai suka ce in rubuto takarda, sai suka ce in ci gaba da aiki.

 Kun riga kun fara aiki kafin ace ku dakata?

kwarai kuwa, ai mu kafin mu fara kamar yadda na fada maka da amincewa muka fara, yanzu haka mun kashe  kudi a wajen da bai yi kasa da Naira dubu 300 ba.

Da yake yanzu an umurceku ku dakata wane mataki za ku dauka?

Yanzu dai za mu mika kokon bararmu ga masu garin. Mu dai ba kowa ba ne, ina gani wannan abu ne da ya kamata a karfafemu akai, domin a makwaftanmu ana bai wa nakasassu sama da 200 aiki, wasu 150, amma mu nan Bauchi babu komai. Amma na san shi Mai girma Gwamnan Bauchi Mohammed Abubakar Esk Makama Babba mai tausayin talakawa ne, amma dai ba mu san ta yaya za mu iya kaiwa gare shi ba, mun sha zuwa gidan gwamnati da nufin mu gan shi sai a dauka bara muka zo yi a hanamu isa gareshi. Ni dan Bauchi ne, kuma a Bauchi nake,  Bauchi garin Yakubu, Bauchi garin Sulaimanu, Bauchi garin Sarki Rilwanu, garin shugaban fafutukar ‘yanci wato Sa Abubakar Tafawa balewa da Mallam Sa‘adu Zungur. 

Saboda me ba ta aiki?

Misalin da zan ba ka, dawowata daga kasar Malesiya inda na yi karatuna ke nan, na dawo cikin kasar nan, cikin jihar nan akwai damar da za a tallafa wa karatun mutane 200. Shi wannan damar tallafin karatu sahihi daga gwamnatin kasar Sin, wato China aka samo, dama ce wacce ita Gwamnatin China za ta bai wa dalibanmu kusan 200 tallafi. Ba wai tallafin da za ka bada kaso kaza a cika maka kaza ba. A’a wanda ga baki daya ne za a dauki nauyin mutum, amma kun san abin mamaki da ban takaici? Kun ga wannan takardar da ke hanuna (ga shi ku gani) takardar neman izinin ganawa ne sun fi guda 15, domin mu samu mutanen gwamnati da za a rubuta yarjejeniyar fahimtar juna wato ‘Memorandum Of Understanding’ na rantse muku da Allah ba ku bina bashin rantsuwa.

 Idan an kammala aikin ko da mutane nawa za ku fara aiki?

A karon farko dai za mu fara ne da nakasassu a kalla 10, domin ba na son na dauko abin da ba zai yiwu ba, kawai dai ƙoƙari ne da kuma yadda na sa abin a raina. Bayan wannan masana’antar da na ke shirin budewa, na ce ma wadansu daga cikin nakasassun mu su je su rubuto sana’ar dogaro da kai wadda ba ta da tsada sosai, sai ni kuma in ga ta yadda zan taimaka musu domin su samu jari. Su kuma wadannan mutane 10 kowannensu duk wata za mu rika biyansa Naira dubu 18.

Kun samu nasarar kammala wannan aikin in abin da ba a fata ya zo ya dakatar da aikin masana’antar ya za ku yi?

To! Sai mu bar wa mutanen garin mu mun yi namu. Mu dai ‘ya’yan jihar ne. Idan ka tashi daga nan ka je titin Wunti za ka gaskata abin da na ke fada maka, za kuma ka gane sosai, babu wanda zai so a ce kullum yana bara. Hannun da tke kasa kullum yana ƙasa, hanun da ke sama kullum shi ne a sama.

Kamar A Jihar Yobe idan nakasashshe zai yi karatu a makarantar Gwamnati Kyauta ne Ko yaya batun yake a Jihar Bauchi

Eh to, yanzu haka dai akwai makarantar  Kwalejin Ilimi da ke Azare, wacce aka maida ita kwalejin Tunawa da Marigayi Aminu Saleh idan nakasashe zai yi karatu a wajen to kyauta ne, amma wannan shirin bai zo cikin gari ba, muna kara yabo da godiya wa shugaban kwalejin Azare.

 To a Azare ne gwamnatin jihar ke daukar nauyin kowa?

Gaskiya wannan kam ban sani ba, ni dai abin da na sani a kwalejin ilimi ta Azare matukar kai nakasasshe ne, kuma kana son karatun to kyauta ne za ka yi karatu a makarantar.

Wane kira gareka ga gwamnati don nakasassu su ci gajiyar dimokuradiyya?

Muna kira da babban murya gwamnati ta dubemu da idon rahama, yanzu maganar da na ke maka babu inda nakasasshe zai je ya yi karatu cikin kwanciyar hankali. ATBU din, babu ajin da zai iya shiga kalubalen da muke fuskanta na da yawa. Muna dai son gwamnatin jihar nan ta jikanmu ta tausaya mana, ta yi mana abubuwan da suka kamata, domin muma mu san ana yi da mu a cikin harkokin mulkin ƙasa. Doka muke son a yi mana mu zama daidai da kowa a kasar nan.

A Kudu nakasasssu ba sa bara, amma a yanki Arewa ake yin barace-barace?

Ba komai ba ne illa rashin kulawar shugabaninmu da shugabanin addininmu da masu fada ajin cikin al’ummar mu. Su ne kawai babbar wannan matsalar kuma su ne suke jawo irin wadannan matsalolin. Yanzu ka taba jin wani malamin da ya fito yana magana a minbari yana cewa ku taimaka wa wadannan da sana’a ba da sadaka ba? ko kuma ka ji an ce an zo an yi wata gidauniya domin taimaka wa nakasassu?. Misalin da na baka, a Ikko  Jihar Legas mutane 250 suka dauka aikin gwamnati, a Arewa mutane nawa ka ji an ɗauka aiki? Yanzu ga shi mu mun tashi da kanmu  muna kokarin samar da aikin wasu suna neman hanawa. Allah ya sa wannan kiran da muka yi ya shiga kunnuwan wadanda muka yi da su, domin muma mu zama kamar kowa a cikin al’umma. Wannan dokar da muke ta maganar a tabbatar mana da ita muna fatan ganin tatabbata.

 
 

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna