Za mu gudanar da zaben fitar da ’yan takara a watan Mayu —APC 

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce za ta gudanar da zabukan fitar da ’yan takara a mukamai daban-daban a watan Mayun 2022. Wannan dai n zuwa ne makonni bayan da jam’iyyar da gudanar da Babban Taronta na kasa inda ta zabi tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugabanta na […]

Za mu gudanar da zaben fitar da ’yan takara a watan Mayu —APC 

Sabon Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce za ta gudanar da zabukan fitar da ’yan takara a mukamai daban-daban a watan Mayun 2022.

Wannan dai n zuwa ne makonni bayan da jam’iyyar da gudanar da Babban Taronta na kasa inda ta zabi tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugabanta na kasa.

Jam’iyyar ta ce za ta fitar da dan takarar shugaban kasa ranar 30 ga watan Mayu.

Za a fara zabukan ne da na ’yan Majalisar Dokoki na jiha a ranar 17 ga Mayu, yayin da na ’yan Majalisar Wakilai zai biyo baya ranar 19, sai kuma na ’yan Majalisar Dattawa ya gudana a ranar 21 ga watan na Mayu.

Zaben fitar da ’yan takara a mukamin gwamna zai gudana ne ranar 24 ga watan na Mayu.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna