Za mu gyara ‘bohol’ 25 a kan N1.2bn —Gwamnan Sakkwato

Za a kashe Naira miliyan 48 wajen gyaran duk rijiyar burtsatse guda daya.

Za mu gyara ‘bohol’ 25 a kan N1.2bn —Gwamnan Sakkwato

Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmad Aliyu

Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, na shan suka kan aikin da bayar na gyaran rijiyoyin burtsatse 25 a kan kudi Naira biliyan daya da miliyan 200.

Jakan na nufin za a kashe Naira miliyan 48 a kan kowace rijiyar burtsatse guda daya.

Jama’a na suka gwamnan kan aikin da ya sanar cewa ya bayar na gyara rijiyoyin burtsatse 25.

Bidiyo sanarwar aikin rijiyoyin burtsatsen da ke yawo a kafofofin sada zumunta ya ba baya da kura, inda jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu.

Wasu da daman sun bayyana  cewa kwangilar ta yi tsada wasu kuma suna shagube a kan aikin.

Honarabul Abdullahi Hassan, ya yi shagube kan kwangilar inda ya nemi mutane da cewa, su nema masa kwangilar gyaran bohol daya.

Bello Muhammad ya ce, “kwangilar gyara bohol daya a kan kudi naira miliyan 48 ba abu ne da yake kama hankali ba.

“ya kamata gwamnati ta rika lura musamman da halin matsin rayuwa da ake ciki a kasar nan.”

Ya yi kira ga “gwamna ya rika duba halin da ake ciki, mutanen da za a gyarawa bohol suna bukatar abinci da magani da hanya.

“Kudin da aka ware a zaton da muke da shi, suna iya samar da abu biyu a cikin abin da ake bukata.

“Amma a kashe makudan kudin a gyaran bohol kamar an barnata kudin.”

Kabiru Ahmad ya ce, “Na kalli bidiyon, domin da aka fada min ban yarda ba, sai da gani da kaina, a gaskiya wannan ita ce kwangila mafi tsada da na sani an bayar a gwamnati.”

Ya ce, “ko samar da bohol da wuya ya wuce a kashe Naira miliyan 10, amma a ce za a yi gyara a miliyan 48, ya kamata gwamnati ta lura a gaba, gaskiya nan an yi kuskure a tunanin da nake da shi.”

Amma daga bisani, Kwamishinan Muhalli na Jihar Sakkwato, Nura Shehu Tangaza, ya yi karin haske kan wani bidiyo.

A cewarsa, sabbin rijiyoyin burtsatse 25 ne za a gidan a kan kuɗi Naira biliyan 1.2, ba gyara ba.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka