Za mu habaka harkar noma – Aliyu
Karamar Hukumar Birnin Abuja ta raba takin zamani ga manoma a yankin, wanda aka gudanar a makon jiya. Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Abdullahi Adamu Candido ne ya kaddamar da raba takin ta hannun kansila mai wakiltar mazabar Wuse Honorabul Aliyu Mathias wanda ya rarraba taki sama da buhu 100 ga manoman yankin. Ya yi kira […]
Karamar Hukumar Birnin Abuja ta raba takin zamani ga manoma a yankin, wanda aka gudanar a makon jiya. Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Abdullahi Adamu Candido ne ya kaddamar da raba takin ta hannun kansila mai wakiltar mazabar Wuse Honorabul Aliyu Mathias wanda ya rarraba taki sama da buhu 100 ga manoman yankin. Ya yi kira ga wadanda suka samu takin su yi amfani da shi domin samun kyakyawar yabanya a gonakinsu, ya kuma gargade su kan kada su sayar da takin, su tsaya su ba da gudunmawarsu ga shirin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na habaka noma a kasar nan.
Mista Aliyu ya gode wa, Alhaji Abdullahi Candido kan wannan karamci da ya yi wa al’ummar mazabarsa ta Wuse na samar musu da takin zamanin a lokacin da suke bukatarsa. Ya ce hakika al’ummar mazabar Wuse sun amsa kiran da Shugaba Buhari ya yi na komawa gona, don haka ba da wannan taki, somin tabi ne wajen samar da abubuwan da za su inganta rayuwar al’ummar mazabarsa. A jawabin Shugaban Jam’iyyar APC na Wuse, Alhajui Salisu Abubakar Baure ya gode wa Alhaji Abdullahi Adamu Candido da Mista Aliyu Mathias domin ba wa al’ummarsu takin, wanda ya ce hakika zai taimaka wajen bunkasa harkar noma a yankin. Sai ya shawarci wadanda suka samu takin su yi amfani da shi domin samun ci gaba.
Wadanda suka samu takin sun gode wa kansilan nasu domin wannan kokari da ya yi musu kuma sun yi alkawarin ba za su ba shi kunya ba. Fiye da manoma 100 ne suka amfana daga rabon takin.