Za mu hana barayin gwamnati takara a 2019 – EFCC

Shugaban Hukumar EFCC a sashen Kudu maso Yamma Alhaji Abdulrasheed Bawa ya ce ranar 9 ga Disamban kowace shekara da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a matsayin ranar Dimokuradiyya ta zo daidai da lokacin da Hukumar ta EFCC take kokarin ganin ta hana barayin gwamnati tsayawa takarar mukamai a babban zabe mai zuwa. Ya fadi […]

Za mu hana barayin gwamnati takara a 2019 – EFCC

Shugaban Hukumar EFCC a sashen Kudu maso Yamma Alhaji Abdulrasheed Bawa ya ce ranar 9 ga Disamban kowace shekara da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a matsayin ranar Dimokuradiyya ta zo daidai da lokacin da Hukumar ta EFCC take kokarin ganin ta hana barayin gwamnati tsayawa takarar mukamai a babban zabe mai zuwa.

Ya fadi haka ne a ranar Litinin lokacin da yake zanta a da Aminiya a Ibadan jim kadan bayan kammala wani gangami da hukumar ta shirya inda ta gayyaci hukumomin soja da ’yan sanda da kwastam da na shigi da fici da kungiyoyin kare hakkin dan Adam domin gudanar da tattaki a cikin birnin Ibadan domin girmama ranar a Najeriya.

Ya ce, “Kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 9 ga Disamban kowace shekara a matsayin ranar yekuwar dimokuradiya a duniya, shi ya sa Hukumar EFCC ta shirya gangamin don mu kara tunatar da ’yan Najeriya cewa cin hanci da rashawa babbar matsala ce da dole ne mun yake ta kuma mu fatattake ta daga cikin al’umma.”

Abdulrasheed Bawa wanda ya nuna gamsuwarsa kan yadda jama’ar gari suka rika fitowa suna sauraren yekuwar yaki da cin hanci da rashawaya ce, “Taken Ranar Dimokuradiyya na bana shi ne ‘Say No To Corruption’ wato kowa ya ce A’a ga Cin hanci da Rashawa). Kuma idan ka ambaci wannan kalma ‘a’a to ka tsaya kuma ka dage a kanta. Hukumar EFCC ta yi maraba da wannan rana saboda kamar yadda kowa ya sani ne cewa nan da ’yan kwanaki kadan za a yi babban zaben shugabanni a Najeriya. Hukumarmu tana so ta yi amfani da wannan dama wajen hana tsayawa takara ga mutanen da suka sace kudin gwamnati a baya suka dawo yanzu suna so su sake rike mukaman shugabancin al’umma. EFCC tana bakin cikin wannan lamari da ba za ta amince ya sake faruwa ba,” inji shi.

Wakilin Aminiya na cikin daruruwan mutanen da suka rike rubutattun kwalaye suka yi jerin gwanon suka zagaya sassan birnin Ibadan domin girmama ranar ta dimokuradiyya ta bana, inda aka yi doguwar tafiya tare da yekuwa ga jama’a su guji aikata duk abin da ya yi kama da cin hanci da rashawa da yake bata sunan Najeriya a kasashen duniya.

Shugabannin kungiyoyin kare hakkin dan Adam a karkashin jagorancin Alhaji Abdulrasheed Bawa sun yada zango a kusa da Coco House gini mafi tsawo na farko a Najeriya da ke Dugbe a birnin Ibadan, inda suka yi jawaban fadakarwa ga jama’a cewa EFCC ita kadai ba za ta iya cimma burinta ba, sai da goyon bayan jama’a musamman wajen bayar da labarin dukan ’yn siyasa da ma’aikatan gwamnati da suke wasoso da kudaden jama’a.