Za mu inganta rayuwar matan Jihar Kebbi – Zainab Bagudu
Matar Gwamnan Jihar Kebbi Dokta Zainab Abubakar Atiku Bagudu ta ce gwamnatin jihar ta yi shiri na musamman don inganta rayuwar matan jihar. Jami’ar Hulda da ’Yan jarida ta matar Gwamna Hajiya Binta Abdulhamid ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da wakilinmu na Jihar Kebbi.Matar Gwamnan ta ce, nasarar da Jam’iyyar APC […]
Matar Gwamnan Jihar Kebbi Dokta Zainab Abubakar Atiku Bagudu ta ce gwamnatin jihar ta yi shiri na musamman don inganta rayuwar matan jihar.
Jami’ar Hulda da ’Yan jarida ta matar Gwamna Hajiya Binta Abdulhamid ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da wakilinmu na Jihar Kebbi.
Matar Gwamnan ta ce, nasarar da Jam’iyyar APC ta samu da kashi 85 cikin 100 a zaben da ya gabata, mata sun taka rawa a kai, “Don haka ba ma a Jihar Kebbi ba; a kasa baki daya, muna iya bugun kirji mu ce wannan gwamnatin ta mata ce, don mu ne masu rinjayen a kuri’un da aka kada,” inji ta.
Ta shaida wa matan Jihar Kebbi, za su bullo da shirye-shiryen bunkasa rayuwar mata wajen koya musu sana’o’i don su dogara da kansu da kuma ba su magunguna kyauta a asibitocin mata da kananan yara da ake da su a jihar. Kuma duk inda ake da gibi a bangaren kiwon lafiya, za su yi kokari su ga sun taimaka wa mata wajen karatun aikin lafiya.
Sai ta yi kira ga matan jihar su ci gaba da ba sabuwar gwamnatin goyon baya da addu’o’i don ta sauke nauyin da ke kanta na alkawarin da ta dauka a lokacin yakin neman zabe.