Za mu iya kawar da bata-gari a Gombe – Sarkin Baka

Sarkin Bakan Bolari, Rabi’u Ibrahim (Baushe) ya bayyana cewa za su iya kawar da bata gari daga Jihar Gombe. Baushe, wanda mafarauci ne da ya shafe sama da shekara 30 yana harkar farauta da harbi, ya bayyana haka ne a yayin wani rangadi. A zantawarsa da Aminiya a Gombe, ya bayyana ayyukan nasu na maharba […]

Za mu iya kawar da bata-gari a Gombe – Sarkin Baka

Sarkin Bakan Bolari, Rabi’u Ibrahim (Baushe) ya bayyana cewa za su iya kawar da bata gari daga Jihar Gombe.

Baushe, wanda mafarauci ne da ya shafe sama da shekara 30 yana harkar farauta da harbi, ya bayyana haka ne a yayin wani rangadi.

A zantawarsa da Aminiya a Gombe, ya bayyana ayyukan nasu na maharba da cewa suna yaki ne da bata-gari da ke cikin Jihar Gombe da suka hada da dakile barayin da suke tare kan hanyoyi da masu garkuwa da mutane da sauransu.

Ya yi amfani da wannan damar ya gode wa mai martaba Sarkin Gombe da Gwamnan Jihar Gombe na yadda suke taimaka masu wajen gudanar da ayyukansu wajen yaki da wadannan bata-gari.

Sannan sai ya ce yana mai kara neman hadin kan jami’an tsaro da su hada kai tare don ci gaba da samar wa al’ummar Jihar Gombe kwanciyar hankali da zaman lafiya. Daga nan sai ya yi fatan jama’ar Gombe za su ci gaba da yi musu addu’a don gamawa lafiya da kuma samun kariya daga sharrin masharranta.