Za mu iya mallake Afirka ta Yamma ta hanyar noma – Minista
Ministan Gona da Raya Karkara, Alhaji Muhammed Sabo Nanono da Minista a Ma’aikatar, Alhaji Mustapha Shehuri sun sha alwashin maida Najeriya cibiyar kayan gona ta yadda za ta tsere wa tsararta a Yammacin Afirka. Da suke yi wa ma’aikatansu jawabi a hedkwatar ma’aikatar da ke Abuja bayan kama aiki, Minista Sabo Nanono, ya ce Najeriya […]
Ministan Gona da Raya Karkara, Alhaji Muhammed Sabo Nanono da Minista a Ma’aikatar, Alhaji Mustapha Shehuri sun sha alwashin maida Najeriya cibiyar kayan gona ta yadda za ta tsere wa tsararta a Yammacin Afirka.
Da suke yi wa ma’aikatansu jawabi a hedkwatar ma’aikatar da ke Abuja bayan kama aiki, Minista Sabo Nanono, ya ce Najeriya za ta iya mallake Afirka ta Yamma gaba daya ta hanyar noma.
“Noma na daya daga cikin abubuwan da ke rike damu a kasar nan tuntuni kuma ina ganin shi ne abin da ya kamata mu habaka sosai. Abin da nake so ku gane shi ne sau da yawa mutane na guje wa harkar noma alhali ba su san irin muhimmancin da noma ke da shi wajen ci gaban kasar nan ba.”
“Ina tabbatar muku cewa idan muka hada kanmu, muka ci gaba da samar da kayan noma ba kama hannun yaro, da sannu za mu mamaye tare da mallake dukkan kasashen Yammacin Afirka ba tare da harba harsashi ko wani makami ba. Saboda yawancin kasashen suna dogaro da abin da muke samarwa ne a nan. Don haka noma abu ne mai matukar muhimmanci hatta ga harkokin tsaron cikin gida, don haka duk wani abu da zai taimaka mana wajen bunkasa harkar ya zama dole mu aiwatar da shi, wannan na daya daga cikin manufofina,” inji sabon Ministan.
Alhaji Nanono wanda ya kasance a cikin harkar kasuwancin kayan noma tun 1973, ya ce akwai sirruka da yawa a fannin noma a kasar nan, inda ya bukaci masu kaurace wa harkar su sake tunani. “Yawancin mutane na guje wa noma saboda wasu dalilai; amma ni na yanke wa kaina shawarar zama a cikinta saboda wasu dalilai masu amfani,” inji shi.
Sai ya kara da cewa ma’aikatarsa na daya daga cikin manyan ma’aikatu masu muhimmanci a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, inda yake bukatar duk hadin kai da goyon baya.
Sababbin ministocin sun sha alwashin aiwatar da shirye-shirye da kudirorin Shugaba Buhari game da burinsa na yalwata kasa da abinci, wanda hakan zai ba kasar nan damar dogara da kanta wajen abinci tare da samar wa kasar nan da arziki a wannan fanni.