Za mu kafa gwamnatin Musulunci a Katsina —NNPP
NNPP ta yi alkawarin soke harajin da aka dora wa takawa a Jihar Katsina.
Jam’iyyar NNPP ta yi alkawarin kafa ingantacciyar gwamnati wadda za ta tafi a kan tsarin Musulunci idan ta ci zaben Gwamnan jihar Katsina da ke tafe.
Mataimakin dan takarar gwaman jihar na Jam’iyyar NNPP, Muttaqa Rabe Darma, ne ya sanar da haka tare da cewa gwamnatinsu za ta soke harajin da aka dora wa takawa a Jihar Katsina.
- Zan biya diyyar mutanen da ’yan bindiga suka kashe a Katsina – Dan takarar Gwamna
- Tsaron Katsina: Za mu dora daga inda Masari ya tsaya —APC
Ya yi alkawarin ne a Zauren Al’Umma da kafafen yada labarai na Media Trust da sauransu suka shirya domin ganawa da ’yan takarar gwamnan jihar a Katsina.
Ya yi jawabin ne da yake wakiltar dan takarar gwamna na jam’iyyarsa, Injiniya Nura Khalil.
Ya shaida wa taron cewa matsalolin Najeriya suna da alaka ta kai-tsaye da rashin ingantacciyar gwamnati me kyakkyawan tsari.
Ya ce a karkashin gwamnatinsu, za su bunkasa sha’anin kudin shiga ta yadda abin da jihar za ta samu daga Gwamnatin Tarayya ba zai wuce kashi 20 cikin 100 ba na kudin shiga.
Darma ya bayyana cewa za su cimma hakan ba tare da dora wa talaka haraji ba.