Za mu kafa kwamitin ƙayyade farashin kayan abinci — Kashim Shettima

Shettima ya ce za a ɗauki wannan matakin ne a yunƙurin daƙile hauhawar farashin kayayyakin masarufi.

Za mu kafa kwamitin ƙayyade farashin kayan abinci — Kashim Shettima

Kayan Abinci

Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyyar kafa kwamitin ƙayyade farashi da bijiro da hanyoyin samun yalwar kayan abinci abinci a kasar.

Mataimakin Shugaban Kasar Kashim Shettima ne ya sanar da hakan a ranar Talata a lokacin wani taron kwana biyu kan sauyin yanayi da abinci.

Shettima ya ce za a ɗauki wannan matakin ne a yunƙurin daƙile hauhawar farashin kayayyakin masarufi.

Mataimakin Shugaban Kasar ya ce kwamitin zai mayar da hankali wajen kula da daidaita farashin hatsi da bullo da hanyoyin wadata kasar da kayan abinci.

Sai dai gwamnatin ba ta bayyana ainihin lokacin da za ta kafa wannan kwamitin ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsaloli na tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.

Hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ta jawo zanga-zanga a wasu sassan ƙasar waɗanda suka haɗa da Neja da Kano.

Sai dai gwamnatin ta sha nanata cewa tana iya ƙoƙarinta wurin ganin ta shawo kan matsalar inda ɗaya daga cikin matakan da ta ɗauka har da na bayar da umarnin fitar da dubban buhunan hatsi daga baitul-malin ƙasar domin rage yunwa a ƙasar.