Za mu kai gwamnatin Oyo kotu kan kafa dokar hana kiwo – Bayari

Kwanakin baya ne Gwamnatin Jihar Oyo ta yi yunkurin kafa dokar hana kiwo a jihar, kamar yadda jihohin Benuwai da Taraba suka yi. Kan haka wakilinmu ya tattauna da Shugaban Kungiyar Ci gaban Al’ummar Fulani ta Najeriya ta Gan Allah, Alhaji Sale Bayari, wanda ya je gaban Majalisar Dokokin  Jihar,  ya gabatar da kukan Fulani […]

Za mu kai gwamnatin Oyo kotu kan kafa dokar hana kiwo – Bayari

Kwanakin baya ne Gwamnatin Jihar Oyo ta yi yunkurin kafa dokar hana kiwo a jihar, kamar yadda jihohin Benuwai da Taraba suka yi. Kan haka wakilinmu ya tattauna da Shugaban Kungiyar Ci gaban Al’ummar Fulani ta Najeriya ta Gan Allah, Alhaji Sale Bayari, wanda ya je gaban Majalisar Dokokin  Jihar,  ya gabatar da kukan Fulani kan wannan yunkuri:

 

Kwanakin baya mun samu labarin ka je gaban Majalisar Dokokin  Jihar Oyo kan kokarin da gwamnatin jihar ke yi na kafa dokar hana kiwo a jihar, me ka shaida wa majalisar?

To wannan dokar hana kiwo da ake son kafawa a Jihar Oyo,  ta zo mana da ba-zata kuma ta zo mana da mamaki. Don haka lokacin da muka samu wannan labari, sai muka je muka samu tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo muka roke shi  ya sa baki kan wannan yunkuri da ake yi. Domin idan aka kafa wannan doka, al’ummar Fulani za su shiga bala’i a jihar. Saboda duk Fulani makiyaya da suke jihohin Yarbawa guda shida, kashi 50 cikin100 suna jihar  ce. Saboda yawan jihar da  yawan wuraren kiwon da take da su.

Domin jihar tun lokacin su marigayi Sardauna aka je aka kafa wuraren kiwo sama da eka dubu 30. Ka ga wannan ya nuna cewa tun lokacin su Sardauna, an san muhimmancin kiwo a jihar. Don haka muka roki Cif Obasanjo, muka ce ya hada mu da masu fada-a-ji a jihar. Domin mu roki a dakatar da yunkurin hana kiwo a jihar. Idan kuma ya zama dole a yi dokar, to a yi dokar yadda ta dace ta yadda al’ummar Fulani ba za su cutu ba. Don haka muka je gaban Majalisar Dokokin Jihar muka gabatar da koke-kokenmu, kan yadda muka ga dokar. Saboda yadda muka ga dokar ta yi niyya ce ta kawar da duk wani Bafulatani makiyayi a jihar kamar yadda aka yi a Jihar Benuwai.

Wato ana son a rabe da guzuma ce a harbi karsana. A ce an kafa dokar ce domin a samu zaman lafiya a tsakanin makiyaya da manoma. Idan zaman lafiya ake so tsakanin makiyaya da manoma, ai  ba fitar da makiyaya za a yi ba. Abin da ya kai mu gaban majalisa ke nan, muka kai kukanmu  cewa wannan doka ba za mu amince da ita ba. Saboda a ce a wannan zamani kana da shanu 50, a ce ba za ka fita ka nemi ciyawar Allah ka ciyar da su ba. Sai dai ka je ka yi hayar gona ko daji ka katange, ka nemo ruwa ka nemo musu abincin da za su ci, nawa za ka kashe? Don haka muka kai musu kuka amma suka ki yarda.

Ganin cewa gwamnatin jihar ba ta da niyyar dakatar da kudirin, wane mataki  kuke shirin dauka kan al’amarin?

To yanzu muna shawarwari kan wannan al’amari. Kuma idan ba a dauki mataki ba kan lamarin, za a iya samun matsala  a jihar, kamar yadda aka samu a Jihar Benuwai. Domin yanzu da aka kafa dokar a Jihar Benuwai, an tashi da kwance uwa kwance. Babu manomi babu makiyayi, mutane ne suna nan suna zaman gudun hijira ko’ina a jihar. Yanzu mutane da dama a jihar, ba sa iya zuwa garuruwa da kauyukansu, ba sa iya zuwa gonakinsu. Saboda haka ba ma son Jihar Oyo ta shiga halin da Jihar Benuwai ta shiga, ta yadda za a zo ana haddasa gaba a tsakanin makiyaya da manoma. Wannan abu bai zamo mai dadi ba. Domin Allah Ya hada mu zauna da juna. Saboda haka muna shawarwari kan matakan da za mu dauka. Idan muka ga sun tsaya kan bakarsu, kan lamarin, a matsayinmu na masu bin doka da oda da kundin tsarin mulkin Najeriya, za mu nemi hakkinmu a kotu. Idan kotu ta ce kafa dokar ta yi daidai a hana mu walwala a cikin Najeriya, za mu saurari abin da za a yi. Kamar yadda muka kai karar Gwamnatin Jihar Taraba.

Kuma karar da muka kai Gwamnatin Jihar Taraba, babu wata daukar fansa ko zubar da jini  ko fada a Taraba. Gwamnatin Taraba tana cewa tana shirin aiwatar da dokar, amma har yanzu saboda wannan kara da muka kai kotu, ba a samu abin da ake so ba. Don haka ba za mu yarda a kafa wannan doka ta hana kiwo a Jihar Oyo ba, amma ba ta hanyar rikici ko rigima ba. Za mu ki yarda da wannan doka ce, ta hanyar doka da oda.

Wane sako kake da shi ga Gwamnatin Jihar Oyo da al’ummar Fulani makiyaya a jihar?

Abin da muke fada shi ne ita Gwamnatin Jihar Oyo, idan da gaske take yi kamar yadda take cewa stana son a yi kiwon zamani ne, muna son mu shaida musu cewa babu yadda za a yi kiwon zamani ba a yi noman zamani ba. Domin a noman zamani ne kamar a kasashen Turai mutum daya zai noma hatsi buhu miliyan biyar. Idan ka dauki karmamin wannan manomi zai iya ciyar da shanu miliyan biyu a wata shida ko shekara. Mu kuma yanzu ba mu da irin wadannan manoma a Najeriya. Idan ka daure shanunka me za ka ba su su ci? Don haka abin da muke cewa shi ne idan ana son a yi kiwon zamani a Najeriya to a fara noman zamani tukuna. Idan aka yi noman zamani muka ga yawan abincin dabbobin da za mu samu daga wajen manoma shi ke nan.

Kuma ya kamata kafin a ce za a canja yadda muke kiwo a Najeriya, a dauke mu a kai mu wajen da ake wannan kiwo na zamani, don a koya mana. Ko a gayyato mana wadanda suke wannan kiwo na zamani, su zo nan Najeriya su koya mana. Ko gwamnatocin da suke son a yi kiwo na zamani, su tura ma’aikatansu kasashen da suke kiwon zamani, don su koyo su dawo su koya mana.

Idan ba haka za a yi ba, ya kamata a kyale mu mu ci gaba da kiwon gargajiya da muka saba. Kuma kamar yadda na fada tun farko mun gaya wa Gwamnatin Jihar Oyo cewa, kafa wannan doka ba za ta yiwu ba. Saboda mun ga illar dokar da aka kafa a Jihar Benuwai. Don haka muna kira ga Gwamnatin Jihar Oyo, ta sake tunani kan wannan kudiri na kafa wannan doka a jihar.