Za mu kammala duk ayyukan da Kwankwaso ya faro – Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta kammala dukkan ayyukan da ta gada daga gwamnatin da ta gabata ta yadda al’ummar jihar za su samu ribar dimokuradiyya mai yawa.  Gwamnan ya yi wannan albishir ne a jawabin da ya gabatar ranar Lahadin da ta gabata don cikarsa kwana 100 a […]

Za mu kammala duk ayyukan da Kwankwaso ya faro – Ganduje
Za mu kammala duk ayyukan da Kwankwaso ya faro – Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta kammala dukkan ayyukan da ta gada daga gwamnatin da ta gabata ta yadda al’ummar jihar za su samu ribar dimokuradiyya mai yawa.  
Gwamnan ya yi wannan albishir ne a jawabin da ya gabatar ranar Lahadin da ta gabata don cikarsa kwana 100 a bisa mulkin jihar, inda ya ce dorawa daga inda gwamnatin baya ta tsaya abu ne da ke saurin kawo ci gaba ga al’umma, don haka yana daga cikin manufofin gwamnatinsa ta kammala ayyukan da gwamnatin Kwankwaso ta faro domin amfanin al’ummar Jihar Kano a birni da karkara.
Dokta Abdullahi Ganduje ya ce za a yi aiki da tsarin nan na ‘Tabbatar da Bin kai’da,’ wajen ba da kwangila a jihar domin kawar da cin hanci da rashawa, kuma nan gaba kadan gwamnati za ta gabatar da bukatar haka ga majalisar jihar ta yadda shirin zai zamo bisa doka don inganta aiki. Gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa ta farfado da Hukumar Yaki da cin Hanci domin tabbatar da ana aiki sosai da manufofin yaki da cin hanci inda ya gargadi ma’aikatan jihar kan su kasance masu kauce wa duk abin da zai kai su ga cin hanci da rashawa.
A tsokacin, Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II ya bukaci shugabanni su kasance masu adalci ga al’umma ta yadda al’amura za su ci gaba da tafiya cikin nasara.  Taron ya samu halartar ’yan siyasar jihar da shugabannin al’umma da na kungiyoyi masu zaman kansu.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista